Hasken Shiriya

Hasken Shiriya Babban manufarmu ita ce isar da sakon Musulunci ba tare da la'akari da bambancin fahimta ko mazhaba ba.

LABARI: Ganduje ya kai ziyarar ta'aziyyar Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi a fadar Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Aminu...
05/04/2025

LABARI: Ganduje ya kai ziyarar ta'aziyyar Galadiman Kano Alhaji Abbas Sanusi a fadar Mai Martaba Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero.

Marigayi Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi Bayero tare da Sheikh Dahiru Bauchi a shekarun baya.Muna addu'a Allah ya jad...
05/04/2025

Marigayi Galadiman Kano Alhaji Abbas Sunusi Bayero tare da Sheikh Dahiru Bauchi a shekarun baya.

Muna addu'a Allah ya jaddadawa Galidama rahma, ya karawa Sheikh Dahiru Usman Bauchi lafiya amin.

Kasar Rasha za ta bude ofishin jakadancinta a Yamai, babban birnin Nijar a bana. Ministan harkokin wajen Rasha Sergei La...
05/04/2025

Kasar Rasha za ta bude ofishin jakadancinta a Yamai, babban birnin Nijar a bana. Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ne ya sanar da hakan a Alhamis yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwarorinsa na kasashen kungiyar Sahel da ke ziyara a birnin Moscow, a cewar ActuNiger, wata kafar yada labarai a Nijar.
Karin bayani-

ECOWAS za ta gudanar da taro domin tattauna batun haraji da kasashen AES s**a sanyawa kasashe mambobin kungiyar ta ECOWAS

SAKO SHUGABAN JIBWIS NIGERIA InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un!A madadin kungiyar Izala, Shugaba Sheikh Dr. Imam Abdull...
05/04/2025

SAKO SHUGABAN JIBWIS NIGERIA

InnalilLahi wa inna ilaihi raji'un!

A madadin kungiyar Izala, Shugaba Sheikh Dr. Imam Abdullahi Bala Lau, na miƙa ta'aziyya ga ƴan uwa da iyalai, da sauran yan uwa Ahlussunnah na jahar Bauchi, dama ƙasa baki ɗaya, bisa rasuwar Sheikh Idris Abdul'azeez Dutsen Tanshi, wanda Allah ya ƙarɓi rayuwarsa a daren juma'ar nan. "Mutuwa Rigar kowa!!

Allah ka jikan Dr Idris Abdulazeez Dutsen Tanshi, ka kyautata makwancin sa, ka haɗamu da shi a gidan aljanna firdausi ranar gobe. Allah ka kai haske kabarinsa, Ka gafarta masa kurakuransa, Ka sanya Aljannah ce makomarsa, Ka kyautata bayansa, ka bawa iyalansa dangana ameen

Abdullahi Bala Lau

Wakilan Cibiyar Nazarce-Nazarce kan Afrika sun jagoranci gabatar da sallar idi ƙarama a ƙasashen Africa da dama ciki har...
04/04/2025

Wakilan Cibiyar Nazarce-Nazarce kan Afrika sun jagoranci gabatar da sallar idi ƙarama a ƙasashen Africa da dama ciki harda ƙasar Ghana,Benin,Siriyalon,Senegal da sauransu.

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Mallam Dikko Umar Radda ta amince da sanya kyamarorin dubarudu a duk...
04/04/2025

Gwamnatin jihar Katsina karkashin jagorancin Gwamna Mallam Dikko Umar Radda ta amince da sanya kyamarorin dubarudu a duka fadin jihar domin inganta tsaro.

A cewar jaridar Punch, Shugaban ƙaramar hukumar Danja, kuma shugaban kungiyar ALGON na jihar Katsina, Rabo Tambaya ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi a wurin wani taron ma su ruwa da tsaki da rundunar ƴansandan jihar ta shirya a birnin Katsina.

📸Katsina Post

ALLAHU AKBAR: Jana'izar marigayi Sheikh Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, da ya gudana yanzu haka a filin Idi na Games V...
04/04/2025

ALLAHU AKBAR: Jana'izar marigayi Sheikh Dr Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi, da ya gudana yanzu haka a filin Idi na Games Village a cikin garin Bauchi.

Allah ya jikan Malam da Rahama, Allah ya gafarta masa kura kuransa.

ALLAH SARKI: Bilal-bin-Rabah Babban Sahabi Muhammad Manzon Allah Ne (S) Kuma Shi Ya Fara Kiran Sallah A Musulunci Bilal ...
03/04/2025

ALLAH SARKI: Bilal-bin-Rabah Babban Sahabi Muhammad Manzon Allah Ne (S) Kuma Shi Ya Fara Kiran Sallah A Musulunci

Bilal ibn Rabah, Wani ’Yantaccen Bawa Na Gadon Abyssiniya Ne, Wanda Ya Kasance Sahabin Annabi Muhammad (S).

An Haifi Bilal A Cikin Gidan Bauta A Makka Ga Iyayen Bayi, Hamamah Da Rabah, Mahaifiyarsa Hamamah Ta Kasance Gimbiya Abyssinia (Habasha) Amma Daga Baya Aka K**a Ta Kuma Aka Bautar Da Ita.

Bilal Ya Kasance Daya Daga Cikin Farkon Wadanda S**a Karbi Addinin Musulunci Kuma Makusancin Manzon Allah Annabi Muhammadu (S).

Bilal Ya Jure Azabar Da Ubangidansa Saboda Imaninsa Kuma Daga Karshe Ya 'Yanta Shi, Ana Girmama Bilal Sosai A Musulunci Saboda Imaninsa Mara Kaushi Da Matsayinsa Na Liman Na Farko.

Manzon Allah Muhammad (S) Ne Ya Zabi Bilal Ya Zama Liman Na Farko, Wanda Ke Da Alhakin Kiran Musulmi Zuwa Ga Sallah, Wannan Shine Kabarin Bilal-bin-rabah.

Allah Ya Kara Mana Son Manzon Allah (S).

Sheck Ibrahim imam Abdullahi Nafada media

30/03/2025
Jerin kasashen da za suyi Sallah a gobe Lahadi in Allah ya kaimu.1, Saudiyya 2, Kuwait 3, Qatar4, Bahrain5, DubaiZuwa ya...
29/03/2025

Jerin kasashen da za suyi Sallah a gobe Lahadi in Allah ya kaimu.

1, Saudiyya
2, Kuwait
3, Qatar
4, Bahrain
5, Dubai

Zuwa yanzu sune kasashen da s**a sanar da ganin jinjirin wata a kasar su.

YANZU-YANZU: An Ga Jinjirin Watan Shawwal A Saudiyya; Gobe Lahadi Take Sallah A Saudi.
29/03/2025

YANZU-YANZU: An Ga Jinjirin Watan Shawwal A Saudiyya; Gobe Lahadi Take Sallah A Saudi.

YANZU YANZU | Al'ummar Garin Zariya Sun Gudanar Da Ralin Ranar Girmama Takalmin Annabi ......Ralin Wanda sha'iran garin ...
23/03/2025

YANZU YANZU | Al'ummar Garin Zariya Sun Gudanar Da Ralin Ranar Girmama Takalmin Annabi ......

Ralin Wanda sha'iran garin Zazzau s**a Jagoranta wanann ranar ta lahadi 23 ga watan Ramadan 1446 , ya samu halartar ɗinbin Al'umma musulmai maza da mata yara da manya, wanda s**a fito don nuna cewa, Tabbas Takalmin Annabi yafi kowa mukami a duniyar nan , inda ralin ya gudana a kofar fadan Sarkin Zazzau Amb Ahmad Nuhu Bamalli

Muna rokon Allah ya kara mana son Manzan Allah ya kara hada kan duk kan Yan uwa Musulmi Albarkacin wannan watan Mai alfarma...

Address

Abuja
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hasken Shiriya posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hasken Shiriya:

Share