19/06/2026
📖 DARASI NA FARKO A ILMIN TAJWIDI
الحمد لله رب العالمين، والصلاة والسلام على نبينا محمد ﷺ.
Ya ku masoya Alƙur'ani, mun fara karantar da littafin "مبادئ في علم التجويد" domin koyon yadda za mu karanta Alƙur'ani kamar yadda Allah Ya saukar da shi.
🔹 Menene Tajwidi? Tajwidi shi ne fitar da kowane harafi daga madaidaicin mafitarsa tare da ba shi haƙƙinsa da siffofinsa.
🔹 Menene hukuncin sa? Koyon ilimin Tajwidi Farḍu Kifāyah ne, amma karanta Alƙur'ani ba tare da kuskuren da zai canza ma'ana ba Farḍu 'Ain ne ga kowane Musulmi.
🌹 Duk wanda yake son karatunsa ya yi kyau, ya gyaru, kuma ya yi daidai da karatun Manzon Allah ﷺ, to ya kula da ilimin Tajwidi.
📌 Karatun Alƙur'ani ba kawai karantawa ba ne, ibada ce da take buƙatar a yi ta yadda ya dace.
Allah Ya sanya mu cikin mutanen Alƙur'ani, Ya sauƙaƙa mana koyonsa da aiki da shi.
✍️ Sameen Mu'az A Sunnah TV
📚 Mabādi'u Fī 'Ilmit-Tajwīd