20/07/2025
Assalamu alaikum ya 'yan uwana matasa.
A yau ina so mu tattauna kan wani muhimmin abu: Dogaro da kai.
Dogaro da kai ba wai kawai samun kudi ba ne, amma wata hanya ce ta rayuwa wacce take koya mana daraja, mutunci, da 'yanci. Lokacin da muka koyi yin amfani da basira, ilimi, da ƙwazo domin tallafawa kanmu, muna gina kyakkyawar makoma ba wai a gare mu kaɗai ba, har ma ga iyalanmu, al'ummarmu, da ƙasarmu baki ɗaya.
DAGA KAINE