26/10/2025
Tornadoes ta doke Pillars a wasan farko na Babaganaru
A wani wasa mai ban sha’awa da s**a buga a filin wasa na Muhammad Dikko da ke birnin Katsina a ranar Asabar, kungiyar kwallon kafa ta Niger Tornadoes ta doke abokiyar karawarta Kano Pillars a wasa na farko da sabon kocin Pillars Babaganaru ya buga, wasan ya tashi da ci 2-0.