Hurras Media

Hurras Media Shafin Hurras Media, shafin labarai da rahotonnin muhimman ayyukan Harisawa da na Harka Islamiyya.

An Yi Muzaharar Maulidi ta Ranar 17 a AbujaYau Lahadi, 17 ga Rabi’ul Awwal 1448H, Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ...
30/08/2026

An Yi Muzaharar Maulidi ta Ranar 17 a Abuja

Yau Lahadi, 17 ga Rabi’ul Awwal 1448H, Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) sun gudanar da Muzaharar ranar 17 ga Rabi’ul Awwal, domin tunawa da ranar haihuwar Manzon Allah (S).

An fara Muzaharar ne da misalin ƙarfe 3:30 na yamma, sannan aka kammala ta da ƙarfe 4:00 na yamma. An kammala Muzaharar lafiya, kamar yadda aka fara.

— Hurras Media





17 Rabi'ul Auwal, 1448
30 August, 2026

30/08/2026

Sakon Maulidi:

— Hurras Media

Muna taya al'ummar Musulmi murna da zagayowar ranar Haihuwar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad (S), wanda a mafi ingancin ruwaya an haife shi ne a ranar 17 ga watan Rabi'ul Auwal.

A lokaci guda kuma muna murna da haihuwar jikansa Imam Jafar Assadiq (AS), wanda shi ma aka haife shi a rana mai kamar ta yau.




WASAN SADA ZUMUNCI TSAKANIN HARISAWA DA DANDALIN MATASA— Hurras Media Harisawan Harkar Musulunci almajiran Sayyid Ibrahe...
29/08/2026

WASAN SADA ZUMUNCI TSAKANIN HARISAWA DA DANDALIN MATASA

— Hurras Media

Harisawan Harkar Musulunci almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) da ke Imam Jafar Sadiq (AS) Zone sun buga wasan ƙwallon ƙafa tare da Dandalin Matasan Harkar Musulunci na Rasulul Akram Zone a garin Malam Madori ta jihar Jigawa.

Wasan wanda aka yi yau Asabar 16 ga watan Rabi'ul Auwal, 1448 (29th August, 2026) don sada zumunci da kuma murna da zagayowar ranar Haihuwar Manzon Allah (S).

A yayin wasan, Harisawa sun yi nasarar zura kwallo huɗu a ragar Dandalin Matasa, inda su kuma Dandalin Matasa s**a yi nasarar jefa kwallo daya a ragar Harisawa, inda aka tashi wasan (4:1).

Manufar wasan ba kawai tantance wadanda s**a yi nasara bane, sai don kara kyautata alaƙa mai ƙarfi tsakanin bangarori biyun, tare da nishadantuwa da wasan.

Irin wannan ba shi ne na farko ko na karshe ba, Harisawa sun saba buga wasanni daban-daban tare da bangarori daban-daban na Harkar Musulunci don karfafa alaƙa mai kyau tsakani. Wannan ɗaya ne daga cikinsu.

Allah Ta'ala Ya ƙara haɗa kawukanmu, Ya tabbatar damu karkashin Jagoranmu (H) wanda shi da ya nusar da mu sada zumunci tsakanin junanmu.






16 Rabi'ul Auwal, 1448

Hotuna:Jiya Juma'a, 15 ga Rabi’ul Awwal 1448H (28/08/2026), Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na garin Yabo s**a gud...
29/08/2026

Hotuna:

Jiya Juma'a, 15 ga Rabi’ul Awwal 1448H (28/08/2026), Almajiran Sayyid Ibraheem Zakzaky (H) na garin Yabo s**a gudanar da Muzaharar Maulidin Manzon Allah (S). An fara Muzaharar ne daga Babban Masallacin cikin garin, inda aka rufe a Babban Junction na garin.

— Hurras Media





28 August 2026

Muzaharar Maulud a Garin Ƙwanni— Hurras MediaJiya Juma’a, 15 ga Rabi’ul Awwal 1448H (daidai da 28/8/2026), ƴan uwa Musul...
29/08/2026

Muzaharar Maulud a Garin Ƙwanni

— Hurras Media

Jiya Juma’a, 15 ga Rabi’ul Awwal 1448H (daidai da 28/8/2026), ƴan uwa Musulmi almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky (H) na garin Kwanni da ke jamhuriyar Nijar, sun gudanar da Muzaharar Maulidin Manzon Allah (S), domin nuna murna da farin ciki da haihuwarsa.

An fara Muzaharar ne da misalin ƙarfe 3:30 na yamma inda aka kammala ta da ƙarfe 6:00 na yamma.




29/08/2026

Harisawan Illela Unit, yayin gudanar da Muzaharar Maulidin Manzon Allah (S) a garin Illela, ranar Juma’a, 15 ga Rabi’ul Awwal 1448H (28/08/2026).

— Hurras Media




29 August, 2026

HURRAS FIRE SERVICE SUN GUDANAR DA KARATU A GARIN GOMBE— Hurras MediaSashen Harisawa masu kula da kashe gobara da kuma k...
28/08/2026

HURRAS FIRE SERVICE SUN GUDANAR DA KARATU A GARIN GOMBE

— Hurras Media

Sashen Harisawa masu kula da kashe gobara da kuma kiyaye aukuwarta (Hurras Fire And Safety Service) sun gudanar da karatu na wuni ɗaya a garin Gombe.

Taron wanda aka yi shi satin da ya gabata, inda s**a gana da wakilansu da ke unitotan Gombe da Jalingo da ke Zone ɗin Imam Musa Alkazeem (AS). Zaman wanda aka yi shi don sake kwakkwafe tunanin ma'aikatan da nusar da su yadda ya kamata su gudanar da aikin yadda yake cikin kwarewa ba tare da an samu matsala ba.

Yayin zaman, wakilai daga Central na Fire Service sun samu damar halarta, inda s**a yi jawabai masu jan hankali kan aikin. Ƙarshe aka rufe zaman karfe 1:30pm bayan fara shi 10:00am.




15 Rabi'ul Auwal, 1448
28th August, 2026

Muzaharar Maulud a Garin Illela— Hurras Media Yau Juma’a, 15 ga Rabi’ul Awwal 1448H (daidai da 28/8/2026), Almajiran She...
28/08/2026

Muzaharar Maulud a Garin Illela

— Hurras Media

Yau Juma’a, 15 ga Rabi’ul Awwal 1448H (daidai da 28/8/2026), Almajiran Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) na Da’irar Illela, Jihar Sokoto, sun gudanar da Muzaharar Maulidin Manzon Allah (S), domin nuna murna da farin ciki da haihuwarsa.

An fara Muzaharar ne da misalin ƙarfe 9:00 na safe, inda aka kammala ta da ƙarfe 12:00 na rana.




28/08/2026

Hurras Kaduna Unit, Imam Baƙir (AS) Zone — Maulud 1448/2026.

— Hurras Media




15 Rabi'ul Awwal 1448

CigiyaMuna cigiyar wanda ya yar da wannan jakar a yayin Tattakin Yaumul Arba'een din Imam Husaini (AS) na bana da aka gu...
28/08/2026

Cigiya

Muna cigiyar wanda ya yar da wannan jakar a yayin Tattakin Yaumul Arba'een din Imam Husaini (AS) na bana da aka gudanar a Abuja.

A cikin jakar akwai kayayyaki, ciki har da CAMERA DSLR ƙirar CANON, wanda a cikinta an dauki hotunan Arba'een din bana a ciki.

In an samu mai ita, ya tuntubi Saifullahi M. Kabir, sai a faɗa masa inda zai karɓa a Abuja.

— Hurras Media
15 Rabi'ul Auwal 1448 (28/8/2026)

Address

Abuja
900108

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hurras Media posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share