21/09/2025
TA LEKO TA KOMA:
Jami’ar European-American ta fitar da sanarwar musanta digirin girmamawa da aka baiwa fitaccen mawaki Dauda Kahutu Rarara a wani biki da aka gudanar a Abuja, tana mai cewa ba ta da hannu a lamarin kuma ba ta taba ba da izini ba.
A ranar Asabar, a wani biki da aka yi a Nicon Luxury Hotel Abuja, wanda Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda ya halarta, wasu mutane sun ba da lambar digirin girmamawa ga Rarara da wasu mutane uku, suna ikirarin wakiltar jami’ar.
Sai dai a cikin wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na yanar gizo, jami’ar ta ce ta musanta Rarara da duk mutanen da s**a yi ikirarin wakiltar ta, ta kuma bayyana taron a matsayin “na bogi”.
Jami’ar ta ce:
“Ba mu taba ba da izinin gudanar da taron karramawa a wannan wuri ba, kuma an shirya wannan biki ne ta hanyar yaudara ba tare da saninmu ko yardarmu ba.”
Haka kuma ta bayyana cewa babu wani digiri na girmamawa da ta bai wa Dauda Kahutu Rarara, Alhaji Ahmed Saleh Jnr., Mustapha Abdullahi Bujawa da Tarela Boroh, kuma duk wadanda ke da sahihin digiri daga jami’ar ana rubuta sunansu ne a cikin rijistar jami’ar.
Ta ƙara da cewa Musari Audu Isyaku wanda ake kiran “wakilin jami’ar a Arewa” da Idris Aliyu wanda aka ce “mamba ne na Governing Council” duk ba su da ikon wakiltar jami’ar, kuma an soke duk wana matsayinsu da ya danganci jami’ar.
Jami’ar ta ce yanzu haka tana shirin kai ƙara ga hukumomin tsaro a Najeriya domin a bi diddigin masu shirya irin wannan aikin zamba da naƙaltar takardu.