21/05/2025
GWAMNAN JIHAR BORNO YA TONA ASIRI AKAN YAKI DA B0K0 HARAM
Dazu da safe anyi hira da Maigirma Gwamnan jihar Borno Professor Babagana Umara Zulum bayan dawowarsa daga inda Boko Haram suke neman mamayewa a jihar Borno, Gwamnan ya tona asiri tare da ya bayyana gaskiyar abinda yake faruwa
Gwamnan Zulum ya shaida wa duniya ba tare da tsoro ba cewa akwai manyan 'yan siyasa da manyan jami'an sojojin Nigeria wanda suke da hannu da taimakawa kungiyar B0k0 Har@m da kudi da makamai da bayanan sirri
Gwamna Zulum ya bayyana takaicinsa akan yadda Shugaban Kasa Tinubu yake tafiyar hawainiya game da yaki da B0k0 Haram, ya roki Tinubu akan ya dinga sauraran wadanda zasu fada masa gaskiya akan wannan matsala
Gwamna Zulum ya roki Shugaban Kasa Tinubu akan ya dena siyasantar da matsalar tsaron Arewa, ya roki a bawa Sojoji manyan makamai na yaki, domin makaman da suke hannun B0k0 Har@m ya fi na Sojojin da suke fagen daga karfi
Zulum yace ina mai tabbatar muku Sojoji basu da kayan fada na zamani irin wanda 'yan ta'adda suke da shi, domin yanzu 'yan ta'adda na amfani har da fasahar zamani wajan yakar Sojoji da kaddamar da hare-hare
Gwamna Zulum yace ya kamata Shugaban Kasa ya saurari bukatun Sojoji, domin Sojoji sun fi kowa sanin yadda za'ayi maganin ta'addancin nan, za'ayi nasara akan B0k0 Har@m domin kwangila ne, da zaran an cire kwangila da almundahana a cikin ta'addancin za'a kawo karshensa, inji Gwamna Zulum
Ina sauraran bayanan Gwamna Zulum akan bala'in da muke fuskanta sai da na kasa rike hawaye ne, zan tura muku bidiyo a Telegram don Allah ku je ku saurareshi
👇
https://t.me/DattiassalafiyTech
Wallahi jama'a akwai matsala, idan fa bamu tashi tsaye ba kar ku sha mamaki a wayi gari B0k0 Har@m sun kwace Kasar Borno gaba daya, dole kowa ya sadaukar, dole ayi magana, sannan a dage da addu'ah
Wannan yakin ba na Gwamna Zulum bane, na duk wani mutumin Arewa ne, bala'in da yake tunkarar Arewa ba karami bane, mu tashi muyi magana ko da za'a kashe mu
Yaa Allah duk wanda yake da hannu a cikin B0K0 Har@m Allah Ka dauki rayuwarsa, Ka nuna mana karshensu gaba daya