Prof. Ibrahim Ahmad maqari

Prof. Ibrahim Ahmad maqari Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Prof. Ibrahim Ahmad maqari, Digital creator, Abuja.

25/08/2026
Maganar Prof. Ibrahim Ahmad Maqary tana koyar da cewa jahilci ba ya zama hujja a kan ilimi. Mutum mai ƙarancin ilimi na ...
02/08/2026

Maganar Prof. Ibrahim Ahmad Maqary tana koyar da cewa jahilci ba ya zama hujja a kan ilimi. Mutum mai ƙarancin ilimi na iya ganin malami yana kuskure, amma hakan ba lallai ne ya zama gaskiya ba, domin ba shi da cikakken ma'aunin tantance abin da yake hukuntawa.

Don haka, ya dace Musulmi ya yi taka-tsantsan wajen s**ar malamai. Idan wani abu bai fahimta ba, mafita ita ce neman bayani cikin ladabi da tawali'u, ba gaggawar yanke hukunci ko cin mutunci ba.

Allah Ya ƙara mana ilimi mai amfani, fahimta madaidaiciya, da ladabin girmama malamai. Amin.

ZIYARAR TA'AZIYA DA KIRA ZUWA GA HADIN KAN MUSULMI.A Safiyar ranar Asabar 19/07/2026 tawagar kira zuwa ga hadin kan Musu...
19/07/2026

ZIYARAR TA'AZIYA DA KIRA ZUWA GA HADIN KAN MUSULMI.

A Safiyar ranar Asabar 19/07/2026 tawagar kira zuwa ga hadin kan Musulmi, karkashin jagorancin Limamin babban Masallacin kasa dake Abuja, Sheikh Prof. Ibrahim Makari, ta kai ziyara ta musamman zuwa ga tsohon Shugaban Hukumar Alhazai ta kasa, kuma jigo a Kungiyar Izala wato Sheikh Abdullahi Pakistan a gidansa dake birnin Kanon Dabo.

Yayin ziyarar bayan gabatar da ta'aziya na rashin mai dakinsa da yayi, Sheikh Prof. Ibrahim Makari ya bayyana Maksudin Ziyarar inda ya nusar da tarihin irin wannan ziyara tun farkon tarihin Musulunci, da kuma kira zuwa ga hadin kan Musulmi da zaman lafiya.

Sheikh Abdullahi Pakistan ya tarbesu cikin girmamawa tare da bayyana farin cikinsa ga wannan ziyara da fatan zata dore da karfafuwar zumunci, hadin kai da zaman lafiya tsakanin Musulmi.

Cikin tawagar wannan ziyara akwai wakilcin Maluma daga bangarori mabambanta k**a daga Izala, Salafiya, Tijjaniyya, Kadiriyya da sauransu.

ALLAH YA KARBI WANNAN ZIYARA YA KARA DANGON ZUMUNCI.

Ziyarar Kwamiti na Musamman na COUNCIL OF ULAMA ta Qasa zuwa ga Reshen Jihar Katsina inda aka Tattauna Muhimman Batutuwa...
19/07/2026

Ziyarar Kwamiti na Musamman na COUNCIL OF ULAMA ta Qasa zuwa ga Reshen Jihar Katsina inda aka Tattauna Muhimman Batutuwa akan Fafutukar Haɗin Kan Malaman Musulunci da Tsaftace Harkar Wa'azi a Nigeria

CIKIN HOTUNA:Fitattun malamai daga Jami'ar Al-Azhar, Maulana Prof. Ibrahim Maqari (H) da Dr. Muhammad Abdur Rahim Al-Bay...
12/07/2026

CIKIN HOTUNA:
Fitattun malamai daga Jami'ar Al-Azhar, Maulana Prof. Ibrahim Maqari (H) da Dr. Muhammad Abdur Rahim Al-Bayoumi, tare da Dr. Na'eemuddin na Bhera Sharif, sun kai ziyara zuwa Cibiyar Ahlus Sunnah Darul Uloom Mujaddadiyya Naeemiyya, Gulshan-e-Naeemi, Malir, Karachi.
A yayin isowarsu, M***i Muhammad Jan Naeemi Mujaddidi, Babban M***in lardin Sindh kuma jagoran Ahlus Sunnah, tare da Alhaji M***i Muhammad Nazir Jan Naeemi Mujaddidi, da kuma Farfesa Dr. M***i Ubaidullah Jan Naeemi Mujaddidi Al-Azhari, sun yi musu kyakkyawar tarba cike da girmamawa.
Dukkanin malamai biyun sun yi jawabi ga ɗalibai, sannan s**a zagaya tsohuwar ɗakin karatu na cibiyar, wanda ke ɗauke da ɗimbin littattafan ilimi da na ruhi (tasawwufi).

Allah ubangiji yaƙara tsawaita mana kwanakinku Maulana

08/07/2026

Ku zama shaida wallahi inason Bawan Allah nan inajin daɗin kallon sa akoda yaushe rayuwarsa abar koyi ce Allah ya ƙara masa lfy da tsawon rai Albarkacin Annabi S A W 🤲

07/07/2026

Fassarar bayanin professor Ibrahim Ahmad maqari Daga kasar pakistan

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Prof. Ibrahim Ahmad maqari posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share