23/06/2026
"Yara manyan gobe" in ji Malan Bahaushe, sai dai wata ziyara a Sansanonin ‘Yan Gudun Hijira ta nuna akasin hakan:
Ku biyomu ku ji dalili!
Ilimi da Rawar da Al’umma Za Ta Taka ga rayuwar Yara 'ƴan gudun hijira dake Gararamba a Birnin Sokoto - Daga Shugaban Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ) reshen Jihar Sokoto, Usman Mohammed Binji
A yayin da na kai ziyarar aiki da dama a matsayina na ɗan jarida zuwa sansanonin ‘yan gudun hijira (IDPs) da ke cikin birnin Sokoto, musamman sansanonin Ramin Kura da Guiwa Eka, na lura da wani yanayi mai matuƙar tayar da hankali da raɗaɗi.
Duk da irin tallafin jin ƙai da ake bayarwa a waɗannan sansanoni, akwai wata babbar matsala da ba'a cika lura da ita ba, wadda ke shafar yara kanana da rikice-rikice s**a rutsa da su.
Abin da ya fi tayar min da hankali shi ne yadda na tarar da ɗimbin yara maza da mata masu shekarun zuwa makaranta amma ba sa halartar kowace irin makaranta.
Wasu ba sa zuwa makarantun boko, haka kuma ba sa samun ilimin addinin Musulunci. Saboda rashin tsari na ilimi, waɗannan yara suna zaman banza a cikin sansanonin, suna gararamba ba tare da wata manufa ko alkibla ba, ba samun kulawa ko abin da zai amfane su.
Abin da ya fi ɗaga hankali kuma shi ne ganin wasu daga cikin waɗannan ƙananan yara suna yawo a tituna da unguwannin da ke kewaye da sansanonin suna neman abinci ta hanyar barace barace.
Yaran da ya k**ata ace suna cikin ajujuwa suna karatu, ko wasanni da kuma shiryawa makomarsu dake tafe, a maimakon haka suna shafe kwanakin su suna bara domin kawai su rayu.
Ganin waɗannan yara marasa laifi suna miƙa hannayensu domin neman sadaka abu ne mai matuƙar raɗaɗi da bakin ciki. Wannan ba wai kawai yana nuna irin wahalhalun da s**a fuskanta ba ne, har ma yana nuna yadda suke rasa ƙuruciyarsu da mutuncinsu da kuma gurinsu na rayuwa.
Yayin da nake zagayawa a sansanonin tare da tattaunawa da mazauna wuraren, na kasa daina tunanin irin makomar da ke jiran waɗannan yara idan ba'a ɗauki matakin gaggawa ba. Kowace rana da yaro ya shafe ba tare da zuwa makaranta ba, rana ce da ta salwanta ko zata iya haifar da cigabansa.
Duk yaron da aka bari ba tare da kulawa da jagoranci ba, zai fi kasancewa cikin haɗarin faɗawa tarkon cin zarafi, ko cikin yaran bata gari da zasu koya masa munanan dabi'u da zasu yi tasiri a rayuwarsa.
Bisa ga abin da na gani, wannan matsala ta wuce batun rashin abinci ko matsuguni ko wasu buƙatu na yau da kullum. Matsalar tana nuna akwai babban gibi a tsarin ilimi da tarbiyya a cikin sansanonin Ramin Kura da Guiwa.
Duk da cewa ana cigaba da samar da agajin gaggawa to makomar ilimin waɗannan yara da s**a rasa muhallansu na cikin rashin tabbas.
Rashin kula da iliminsu tabbas zai jefa su cikin wani hali, saboda tasirin rikice-rikice s**a haifar da kuma wasu matsalolin zamantakewa da ka iya haifar da mummunan tasiri na dogon lokaci.
Saboda haka, na yi imanin cewa ƙungiyoyin al’umma, musamman ƙungiyoyin addinin Musulunci, suna da muhimmiyar gudummawa da zasu bada wajen taimakawa da cike gibin da ke akwai tare da gwamnati, maimakon jiran gwamnati kaɗai ta magance wannan ƙalubale.
Matsalar ta wuce misali kuma ta yi girman da ta wuce a bar ta a hannun hukumomin gwamnati kaɗai.
Addinin Musulunci ya ba da muhimmanci matuƙa ga neman ilimi, tausayi da kula da marasa ƙarfi, musamman yara, don haka bai k**ata waɗannan ƙa’idoji su tsaya a matsayin magana kawai ba, dole ne a gansu a aikace.
Ƙungiyoyin Musulunci da Malamai da ƙungiyoyin agaji za su iya taimakawa wajen kafa cibiyoyin koyo a cikin sansanonin ‘yan gudun hijira, inda yara za su samu ilimin boko na asali tare da ilimin addini da tarbiyya.
Haka kuma, Malamai masu aikin sa kai da masu ilimantar da al’umma za su iya koyar da karatu da rubutu, ilimin Alƙur’ani, ba da shawarwari da kuma sauya tunani da zamantakewa domin dawo da hankali yaran tare da ƙara musu ƙwarin gwiwa ko.
Al’umma baki ɗaya ma tana da babban nauyi a kanta. Attajirai, masu hannu da shuni, ƙungiyoyin ƙwararru da shugabannin al’umma za su iya tallafa wa shirye-shiryen ilimi ta hanyar bayar da gudummawa, kayan koyarwa, tallafin karatu da kuma ayyukan sa kai. Komi ƙanƙantar gudummawa tana da tasiri, tana iya kawo babban sauyi a rayuwar waɗannan yara.
Daga abin da na gani a sansanonin Ramin Kura da Guiwa Eka, waɗannan yara ba wai sun rasa matsugunansu kawai ba ne, da dama daga cikinsu suna tafiyar da rayuwarsu ba tare da tsari, jagoranci ko kariya ba. Wannan yanayi ya k**ata ya dami kowane ɗan Najeriya.
Idan muka kasa ɗaukar mataki a yau, muna cikin haɗarin samar da wata al’umma da aka hana ilimi da damar da za ta taimaka musu su zama ‘yan ƙasa masu amfani ga al’umma.
Saboda haka, ya zama wajibi ga ƙungiyoyin al’umma, ƙungiyoyin addinin Musulunci da duk masu kishin ƙasa su ɗauki matakin farko, su yi aiki tare da gwamnati da hukumomin agaji domin magance wannan ƙalubale.
Ta haka ne za a iya dawo da mutunci da kyakkyawar makoma ga rayuwar yaran da rikice-rikice s**a shafa a jihar Sokoto.
Waɗannan yara ba su cancanci rayuwa ta tsira da rai kawai ba. Sun cancanci ilimi. Sun cancanci kariya. Fiye da komai, sun cancanci makoma mai cike da damarmaki da manufa da kuma fata nagari.
ATS Hausa na tunatar da sakkwatawa cewa, "Kukan kurciya ma jawabi ne" mu tabbatar mu hada hannu mun samarwa yaran nan makoma ta gari kafin dare yayi mana hausawa s**a ce idan kunne yaji gangar jiki ta tsira.