22/07/2026
DAGA KEBBI STATE GOVERNANCE WATCH
SHUGABANCI MAI HANGEN NESA: SANATA ABUBAKAR ATIKU BAGUDU DA GINA SABUWAR FATA GA MATASAN KEBBI
A duk lokacin da ake magana kan shugabanci nagari, abin da ya fi muhimmanci ba yawan alkawurra ba ne, illa irin tasirin da shugaba ke bari a rayuwar al'umma. Shugaba na gari shi ne wanda ke gina mutane kafin ya gina gine-gine, domin ci gaban al'umma yana ta'allaka ne da inganta rayuwar ɗan Adam.
Sabuwar damar da aka samar wa matasan Jihar Kebbi ta hanyar shirin Football Scouting ba wani abin farin ciki ba ne kawai, alama ce ta irin hangen nesa da jajircewar Mai Girma Ministan Kasafi da Tsare-tsaren Tattalin Arziki na Tarayyar Najeriya, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, CON, wajen gina makomar matasa da kuma samar musu da hanyoyin cimma burikansu.
A yau, duniya ta fahimci cewa baiwar matasa ita ce sabon arzikin kowace al'umma. Duk shugaban da ya zuba jari wajen bunƙasa basirar matasa, yana gina tattalin arziki, yana rage zaman banza, yana ƙarfafa zaman lafiya, kuma yana ɗora ƙasa a kan tafarkin ci gaba mai ɗorewa.
Abin yabawa ne yadda Sanata Bagudu ke ci gaba da amfani da matsayinsa wajen buɗe ƙofofin da matasan Kebbi za su shiga su nuna baiwarsu ga duniya. Wannan ba kawai shiri ba ne, wata manufa ce ta nuna cewa matashin Kebbi yana da abin da zai bayar idan aka ba shi dama.
A Kebbi State Governance Watch, muna kallon irin waɗannan matakai a matsayin ginshiƙan ci gaba da ya kamata a riƙa ƙarfafawa. Lokacin da shugabanni ke fifita damar matasa fiye da kalaman siyasa, suna gina tarihi ne da al'umma za ta ci gaba da tunawa da shi.
Muna yabawa Mai Girma Ministan bisa wannan kyakkyawan yunƙuri, tare da fatan Allah Maɗaukakin Sarki Ya ƙara masa lafiya, hikima, basira da ƙarfin guiwa domin ci gaba da yi wa Najeriya da Jihar Kebbi hidima cikin adalci da hangen nesa.
Muna kuma ƙarfafa matasan da s**a samu wannan dama da su yi amfani da ita cikin ƙwazo, ladabi da jajircewa, domin su zama jakadun alheri ga kansu, ga iyalansu, ga Jihar Kebbi, da kuma Najeriya baki ɗaya.
A ƙarshe, shugabanci na gari ba ya bayyana a cikin jawabai kaɗai; yana bayyana ne a cikin rayukan da aka canja da kuma damar da aka samar. Wannan yunƙuri na ɗaya daga cikin irin matakan da ke tabbatar da cewa akwai shugabanni da ke ganin matasa a matsayin ginshiƙan makomar ƙasa.
.