
09/10/2025
Yanzu Yanzu: Shugaba Tinubu ya Zauna don tattaunawa da Majalisar Koli ta Ƙasa
Shugaban Ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, a halin yanzu yana jagorantar zaman Majalisar Koli ta Ƙasa (Council of State) a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja, inda ake sa ran zai gabatar da sunayen waɗanda zasu maye gurbin kujerar shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC). Zaman, wanda aka fara da misalin ƙarfe 1:29 na rana a yau Alhamis, ya zo ne kwana biyu bayan kammala wa’adin shekaru 10 na Farfesa Mahmood Yakubu a matsayin shugaban INEC, wanda ya ja ragamar shugabancin hukumar a ƙarƙashin gwamnatoci biyu tare da gudanar da manyan zaɓuɓɓuka uku.
Bisa ga jerin ajanda da aka gani kafin zaman ya koma na sirri, Shugaba Tinubu ya gabatar da sunayen mutane uku domin a tantance su, Farfesa Joash Amupitan, Mai Shari’a Abdullahi Mohammed Liman, da kuma Farfesa Lai Olurede. Waɗannan duka masana ne a fannin shari’a da ilimi, kuma za a zaɓi ɗayan su a matsayin wanda zai gaji Mahmood Yakubu domin shugabantar hukumar INEC.
Tsoffin Shugabannin Ƙasa, Janar Abdulsalami Abubakar (mai ritaya) da Janar Ibrahim Badamasi Babangida (mai ritaya), sun halarci zaman ta kafar bidiyo, yayin da ake jiran dakon shigowar tsofaffin shugabannin ƙasa, Olusegun Obasanjo da Goodluck Jonathan.
A cikin wadanda s**a halarci zaman a zahiri akwai Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima; Sakataren Gwamnatin Ƙasa, George Akume; Mai Ba da Shawara na Musamman kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu; Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi (SAN); da Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa, Femi Gbajabiamila. Haka zalika, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio; Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas; da gwamnonin jihohi da dama ko mataimakansu sun halarci taron. Ana sa ran Shugaba Tinubu zai yi jawabi kan tattalin arziki, tsaro da sauran al’amuran ƙasa kafin a mika sunayen da aka zaɓa ga Majalisar Dattawa domin tabbatarwa.