Basira TV

Basira TV BASIRA TV wani gidan talabijin ne na zamani da ke ba da labarai, bayanai, da haske kan abubuwan da ke faruwa a gida da ƙasashen waje.

Gidan talabijin ɗin yana da manufa ta “Idon da ya wuce bayar da labarai kaɗai.”

27/08/2026

Zagayen maulidin fiyayyen Halitta Manzon Allah (S) a Kootanad, dake yankin Palakkad, Kerala, a ƙasar India | Basira TV

Kotu a Iran Ta Bai wa Iraniyawa Dala Miliyan 37 Na Amurka da ta kwaceA wani hukunci mai matuƙar muhimmanci na tarihi, wa...
27/08/2026

Kotu a Iran Ta Bai wa Iraniyawa Dala Miliyan 37 Na Amurka da ta kwace

A wani hukunci mai matuƙar muhimmanci na tarihi, wata kotun ƙasa da ƙasa a Jamhuriyar Musulunci ta Iran ta bayar da umarnin raba kuɗaɗen da aka kwace daga wani jirgin dakon man fetur na Amurka ga majinyatan Iran da ke fama da wata cutar fata mai ƙarancin yaduwa da aka fi sani da “butterfly disease."

A cewar hukuncin, takunkumin da Amurka ta ƙaƙaba ba bisa ƙa’ida ba ya hana waɗannan marasa lafiya samun muhimman magungunan da za su iya ceto rayuwarsu.

Wannan hukunci ya zama karo na farko da Iran ta yi nasarar kwace kadarorin Amurka domin amfanin ’yan ƙasarta, kamar yadda rahoton ya bayyana.

Ƙungiyar Matasan Arewa Ta Nemi Tinubu Ya Naɗa Ganduje Daraktan Yaƙin Neman Zaɓensa Na 2027Wata ƙungiyar matasa mai suna ...
26/08/2026

Ƙungiyar Matasan Arewa Ta Nemi Tinubu Ya Naɗa Ganduje Daraktan Yaƙin Neman Zaɓensa Na 2027

Wata ƙungiyar matasa mai suna Arewa Youths for Good Governance and Development (AYGGD) ta yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya naɗa tsohon Gwamnan Jihar Kano kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a matsayin Daraktan Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC a zaɓen 2027.

Shugaban ƙungiyar, Nura Abubakar, ya ce Ganduje na da ƙwarewar siyasa, sanin tafiyar APC da kuma kyakkyawar fahimta kan siyasar ƙasa, musamman a yankin Arewa, abin da ya ce zai taimaka wa jam’iyyar wajen gudanar da yaƙin neman zaɓe mai inganci.

Ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya aikawa Basira TV a ranar Talata 26 ga watan Agustan 2026. Nura ya bayyana cewa Ganduje ya taɓa jagorantar APC a matsayin Shugaban Jam’iyyar na Ƙasa, sannan ya kasance Gwamnan Kano na tsawon shekaru takwas, inda ya samu damar hulɗa da ’yan siyasa da masu ruwa da tsaki daga sassa daban-daban na ƙasar.

Ya ce ƙwarewar Ganduje wajen siyasar ƙasa da sanin tsarin jam’iyya ya sa ya dace da jagorantar tsarin yaƙin neman zaɓen Tinubu a 2027.

“Muna ganin Dr. Abdullahi Umar Ganduje yana da kwarewa, dabarun siyasa da kuma faɗin alaƙar da ake buƙata wajen jagorantar yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa. Saboda haka muna kira ga Shugaba Tinubu da ya yi la’akari da ba shi wannan muhimmin aiki,” in ji Nura.

Shugaban ƙungiyar ya ƙara da cewa irin wannan naɗin zai iya ƙarfafa tsarin haɗa kan magoya bayan APC da kuma ƙara ƙaimi wajen tunkarar zaɓen 2027.

Ganduje dai ya sha bayyana goyon bayansa ga sake zaɓen Shugaba Tinubu a 2027, inda ya ce babu wani ɗan takara daga Kudancin Najeriya da ya fi Tinubu dacewa da shugabancin ƙasar bayan 2027.

Haka kuma, a baya wata ƙungiya mai suna National Agenda for Tinubu 2027 (NAFT.27) ta gabatar da irin wannan buƙata, inda ta nemi a naɗa Ganduje a matsayin Darakta-Janar na Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Tinubu na 2027, bisa la’akari da ƙwarewarsa da alaƙar siyasa a faɗin ƙasar.

Nura ya yi kira ga Shugaba Tinubu da shugabannin APC da su duba buƙatar tare da ɗaukar matakin da zai ƙara wa jam’iyyar ƙarfi gabanin babban zaɓen 2027.

Editan Leadership Ya Rubuta Littafi Kan Sauyin Zamani A Aikin JaridaBabban Editan Labarai na rukunin kamfanin jaridar LE...
26/08/2026

Editan Leadership Ya Rubuta Littafi Kan Sauyin Zamani A Aikin Jarida

Babban Editan Labarai na rukunin kamfanin jaridar LEADERSHIP, Dr. Sunday Isuwa, ya wallafa wani sabon littafi mai taken “Digital Shift In Nigeria’s Newspaper Industry”, wanda ya yi fashin baƙi kan yadda ci gaban fasaha ke sauya fasalin yadda ake gudanar da aikin jarida, tsarin kasuwanci, da kuma yadda kafafen yaɗa labarai ke cuɗanya da masu karatunsu a Nijeriya.

A cewar wata sanarwa da aka fitar, za a ƙaddamar da wannan muhimmin littafi a hukumance a ranar 29 ga watan Oktobar 2026, da misalin karfe 10:00 na safe a Babban Zauren Taro na Jami’ar NOUN, da ke Jabi, a birnin Tarayya Abuja.

Tsohon Kakakin Majalisar Wakilai, Honarabul Yakubu Dogara, wanda kuma shi ne Shugaban Kamfanin Ba da Lamuni na Ƙasa (NCGC), ne zai kasance shugaban taron, yayin da Mataimakin Shugaban Jami’ar NOUN, Farfesa Uduma Oji Uduma zai yi sharhin littafin. Farfesa Rotimi Olatunji, malami a Jami’ar Jihar Legas kuma shugaban ƙungiyar Malaman Sadarwa ta Kasa, shi ne ya rubuta gabatarwar (foreword) littafin.

Manyan masana da ƙwararru a fagen aikin jarida sun yi matuƙar yaba wa wannan aiki. Farfesa Umaru Pate na Jami’ar Bayero ta Kano ya siffanta littafin a matsayin wanda ya zo a daidai lokacin da ake buƙatar fahimtar irin sauye-sauyen da ke faruwa a masana’antar yaɗa labarai, inda ya bayyana cewa littafin ya taɓo muhimman batutuwa kamar tattara labarai ta amfani da kafofin sadarwa na zamani da kuma yaƙi da labaran karya.

Haka zalika, Farfesa Farooq Kperogi na Jami’ar Kennesaw da ke ƙasar Amurka ya bayyana cewa Dr. Isuwa ya yi amfani da kwarewarsa a aikin jarida da kuma bincike na ilimi wajen fito da yadda jaridun gargajiya s**a koma kan tsarin intanet.

A nasa jawabin, Manajan Darakta na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Malam Ali M. Ali, ya roƙi dukkanin ƙwararru, da malamai, da masu tsara manufofi da su halarci wannan taron ƙaddamarwa.

Ya nuna cewa littafin bai tsaya kawai wajen bayyana tarihin jaridu a Nijeriya ba, har ma ya duba ƙalubalen da ‘yan jarida ke fuskanta wajen daidaita gaggawar fitar da labari da kuma tabbatar da sahihancinsa a wannan zamanin da fasaha ta mamaye komai, wanda hakan zai taimaka wajen samar da madogara ta gari ga ɗalibai da masu nazarin aikin jarida a ƙasar nan.

26/08/2026

Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky Sun Gudanar da Zagayen Maulidin Manzon Allah (SAWW) a Kano

Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun gudanar da zagayen murnar Maulidin fiyayyen halitta, Manzon Allah Muhammad (SAWW), a Kano, inda dubban mahalarta s**a fito domin nuna farin ciki da ƙauna ga Annabi (SAWW). Cikakken rahoton Basira TV.

Yau Ne Ranar Hausa Ta Duniya: Wace Karin Magana Ko Zaurance Ka Fi So?A yau, 26 ga Agusta, ake bikin Ranar Hausa ta Duniy...
26/08/2026

Yau Ne Ranar Hausa Ta Duniya: Wace Karin Magana Ko Zaurance Ka Fi So?

A yau, 26 ga Agusta, ake bikin Ranar Hausa ta Duniya.

BASIRA TV na taya ɗaukacin al’ummar Hausawa da ke faɗin duniya murnar wannan rana, tare da ƙara jaddada muhimmancin harshen Hausa a matsayin harshen da ya haɗa miliyoyin mutane a duniya.

Kawo mana karin magana, zaurance, salon magana ko sara guda ɗaya da ta fi kwanta maka a rai. ❤️

🗣️ Hausa tamu ce, mu riƙe ta, mu raya ta, mu isar da ita ga tsara masu zuwa.

BASIRA TV na yi wa ɗaukacin Hausawa Barka da Ranar Hausa ta Duniya! 🎉🌍

Almajiran Sheikh Zakzaky Sun Tsaftace Garin Zariya Bayan Kammala Zagayen MaulidiBasira TV ta labarto cewa, gamayyar ’yan...
26/08/2026

Almajiran Sheikh Zakzaky Sun Tsaftace Garin Zariya Bayan Kammala Zagayen Maulidi

Basira TV ta labarto cewa, gamayyar ’yan uwa Musulmai almajiran Sheikh Ibrahim Zakzaky sun gudanar da aikin tsaftace garin Zariya a safiyar Laraba, 26 ga Agusta, 2026, bayan kammala gagarumin zagayen Maulidin Manzon Allah ﷺ da aka gudanar a ranar Talata, 25 ga Agusta, wanda ya yi daidai da 12 ga Rabi’ul Awwal.

Kamar yadda s**a saba a shekarar da ta gabata, mahalarta aikin tsaftacewar sun haɗa maza da mata, yara da manya, waɗanda s**a fito domin kwashe shara da tsaftace hanyoyin da aka bi yayin zagayen Maulidin.

An fara aikin ne daga Shatale-talen Babban Dodo, ta hanyar Fadan Zazzau, aka bi ta Durumi, Shalkwata, Kamfage da Bakin Kasuwa, kafin a nufi Karauka.

Waɗannan hanyoyi na daga cikin manyan hanyoyin da mahalarta zagayen Maulidin s**a bi a lokacin gudanar da shi.

A yayin aikin, mahalartan sun rika tsintar tare da kwashe abubuwan da aka yi amfani da su a lokacin zagayen, musamman ledoji da sauran tarkacen da s**a rage a kan tituna.

Al’umma mazauna yankunan da aka gudanar da aikin sun bayyana farin cikinsu tare da yaba wa mahalarta bisa wannan ƙoƙari na tsaftace muhalli bayan kammala taron.

Wasu daga cikin mutanen garin sun kuma yi wa mahalarta addu’a, suna masu bayyana aikin a matsayin wata gudunmawa wajen tabbatar da tsafta da kyawun garin Zariya.

Fuskokin Jami’an ’Yan Sandan Najeriya 10 Da S**a Rasa Rayukansu Suna Yaƙi Da Daruruwan ’Yan Bindiga A KebbiCikakken laba...
26/08/2026

Fuskokin Jami’an ’Yan Sandan Najeriya 10 Da S**a Rasa Rayukansu Suna Yaƙi Da Daruruwan ’Yan Bindiga A Kebbi

Cikakken labarin zai zo daga baya.

26/08/2026

Zagayen maulidin fiyayyen Halitta Manzon Allah (S) a Moroko

FCTA Ta Ci Gaba Da Rushe Gidaje Da Aka Gina A Hanyoyin RuwaHukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta ci gaba da rushe gine...
26/08/2026

FCTA Ta Ci Gaba Da Rushe Gidaje Da Aka Gina A Hanyoyin Ruwa

Hukumar Babban Birnin Tarayya (FCTA) ta ci gaba da rushe gine-gine da wasu gine-ginen da aka gina a kan hanyoyin ruwa da wuraren da zaizayar ƙasa ke bi a sassan Abuja.

Aikin rushe-rushen na daga cikin matakan da hukumomin babban birnin tarayya ke ɗauka domin rage barazanar ambaliyar ruwa da zaizayar ƙasa tare da kare muhalli.

Address

Gwarinpa
Abuja

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Basira TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share