Ajingi Online News

Ajingi Online News Zamun Dinga Kawo Muku Ingantattun Labarai Na Gaskiya Da Gaskiya Kuci Gaba Da Bibiyar Ajingi Online News 🗞️

𝗟𝗨𝗜𝗦 𝗘𝗡𝗥𝗜𝗤𝗨𝗘: "Na kalli wasan Barcelona da Elche gaba daya, kuma da gaske, ina fatan ba za su sayi Julián Álvarez ba.  "...
26/08/2026

𝗟𝗨𝗜𝗦 𝗘𝗡𝗥𝗜𝗤𝗨𝗘:

"Na kalli wasan Barcelona da Elche gaba daya, kuma da gaske, ina fatan ba za su sayi Julián Álvarez ba.

"Domin idan s**a kara Álvarez a wannan kungiyar, zan iya cewa da karfin gwiwa za su iya mamaye kwallon kafa a duniya na tsawon shekaru biyar masu zuwa - ba kawai a wannan kakar wasan ba har ma na gaba ba.

"Wannan kungiyar Barcelona tana da matukar ban mamaki kuma ta zama cikakkiya a yanzu, musamman a karkashin babban Koci kamar Hansi Flick.

"Ba zan yi mamaki ba idan s**a lashe gasar zakarun Turai biyar a jere bayan sun sayi Julián." Haka nake ganin ƙungiyar a gare ni."

☆ Ajingi Online New

Dalilin fushin Lamine Yamal a wasan Barcelona da Elche shine yana baƙin ciki ne game da abin da ke faruwa da Balde.Yana ...
25/08/2026

Dalilin fushin Lamine Yamal a wasan Barcelona da Elche shine yana baƙin ciki ne game da abin da ke faruwa da Balde.

Yana da kusanci sosai da Balde, sai dai kuma Hansi Flick ya ce baya bukatar Balde.

Wannan shine dalilin fushin nasa in ji Sport.

❍ Ajingi Online News

25/08/2026

I got over 40 reactions on one of my posts last week! Thanks everyone for your support! 🎉

Da ɗumi-ɗumi: An rahoto cewa Diego Simeone bai so Julián Álvarez ya buga wasan da Atlético Madrid ta yi da Villarreal ba...
24/08/2026

Da ɗumi-ɗumi: An rahoto cewa Diego Simeone bai so Julián Álvarez ya buga wasan da Atlético Madrid ta yi da Villarreal ba, amma shugabannin Atlético ne s**a tilasta masa ya saka shi a cikin tawagar ƙungiyar.

Manufar Simeone ita ce a jira har zuwa ƙarshen kasuwar musayar ƴan wasanni kafin a dawo da Álvarez cikin tawagar ƙungiyar. Sai dai hukumar gudanarwa Atlético ta dage kan cewa dole ne ya buga wasansu na gida da Villarreal.

An bayyana cewa shugabannin ƙungiyar suna son Álvarez ya fuskanci fushin magoya bayan Atlético Madrid, tare da matsa masa lamba bayan ya ƙi amsar tayin da s**a gabatar masa na ƙarin kwantaragi.

Rahotanni sun ce Atlético ta bai wa Julián zaɓi biyu: ya nemi gafarar magoya bayan ƙungiyar, ko kuma ya amince da komawa wata ƙungiyar ta wajen Sifaniya kan kuɗi €135m. Sai dai Álvarez bai ce komai akan hakan ba, saboda abin da ya fi baiwa muhimmanci a yanzu shi ne komawa Barcelona.

Atlético ta ƙuduri aniyar ci gaba da matsa wa Álvarez da tawagarsa lamba har sai sun amince da ɗaya daga cikin waɗannan zaɓuɓɓuka. A halin yanzu, ƙungiyar bata tunanin barin Julián ya koma Barcelona.

• Ajingi Online News

Full Time 0-5
24/08/2026

Full Time 0-5

Shirin Barcelona na biyu ya fara!Brcelona ta fara neman wasu ƴan wasan gaban, bayan da ƙoƙarinsu na ɗaukar Julián Álvare...
23/08/2026

Shirin Barcelona na biyu ya fara!

Brcelona ta fara neman wasu ƴan wasan gaban, bayan da ƙoƙarinsu na ɗaukar Julián Álvarez ya ƙara zama mai wahala.

🇩🇪 Nicolò Tresoldi (Club Brugge) | €25M
🇦🇷 Lautaro Martínez (Inter Milan) | €85M
🇬🇷 Vangelis Pavlidis (Benfica) | €28M
🇬🇪 Georges Mikautadze (Villarreal) | €30M
🇨🇴 Luis Suárez (Sporting CP) | €80M
🇪🇸 Mikel Oyarzabal (Real Sociedad) | €25M
🇫🇷 Junior Kroupi (Bournemouth) | €70M
🇸🇪 Viktor Gyökeres (Arsenal) | €65M

Ga magoya bayan Barca: Wanne ɗan wasan kuke ganin ya kamata ƙungiyar ta ɗauka? 🤔

• Ajingi Online News

23/08/2026
BOOOOOOOM 💥 - BALDE YA YI BANKWANA DA BARCELONA.Rahotonnin sun tabbatar da cewa Alejandro Balde ya yi bankwana da ma'aik...
23/08/2026

BOOOOOOOM 💥 - BALDE YA YI BANKWANA DA BARCELONA.

Rahotonnin sun tabbatar da cewa Alejandro Balde ya yi bankwana da ma'aikatan Barcelona.

Dan wasan baya cikin tawagar kungiyar da zata buga Wasa da Elche a daren yau.

Ficewar dan wasan ta tabbata bayan da Hansi Flick ya bayyana cewa dan wasan ya nemi kungiya.

❍ Ajingi Online News

SAƘON AL’UMMAR GARIN KWASHI“GYARAN WANNAN MAKARANTA SHINE ƘURI’AR GARIN KWASHI A ZABEN 2027” — Inji wasu daga cikin al’u...
23/08/2026

SAƘON AL’UMMAR GARIN KWASHI

“GYARAN WANNAN MAKARANTA SHINE ƘURI’AR GARIN KWASHI A ZABEN 2027” — Inji wasu daga cikin al’ummar Garin Kwashi, da ke Mazabar Kunkurawa, Ajingi Local Government.

Makarantar Nurul Islam Kwashi Mabuga na fuskantar matsaloli masu tsanani, musamman rashin ingantaccen wajen karatu da matsalar ruwan sama, lamarin da ke kawo cikas ga karatun ɗalibai.

Al’ummar garin sun bayyana cewa gyaran makarantar ya zama babban abin da za su duba wajen yanke shawarar siyasarsu a 2027.

Muna kira ga gwamnati, masu ruwa da tsaki da kuma al’ummar gari da su hada hannu wajen ganin an samar da ingantaccen wajen karatu ga yaranmu.

Ilimi shi ne ginshikin ci gaban al’umma.
Mu ba yaranmu damar samun ilimi cikin aminci da mutunci. 🤲

📍 Kwashi, Mazabar Kunkurawa, Ajingi L.G.A.
📰 AJINGI ONLINE NEWS — Gaskiya Da Gaskiya

22/08/2026

Kukan Kurciya Jawabi Ne

Address

Ajingi
001

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Ajingi Online News posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share