26/01/2026
My 1 year in Digital marketing journey
Alhmdullh
A yau na cika shekara 1 cif a tafiyar da na fara a digital / affiliate marketing.
Na yanke shawarar rubuta wannan ba don nuna show-up ba, sai don in nuna opportunity (dama) da darasin da na koya, domin wani ya samu kwarin gwiwa.
Na fara wannan tafiya ne a January 2025, bayan da na ga sponsored ad a TikTok daga coach dita, Amina Ibrahim. Na shiga class dinta a WhatsApp, daga nan na sayi CMS (Cashflow Mastery System), na fara koya, na fara aiwatarwa, duk da cewa a wancan lokacin ban san komai ba.
A farkon tafiya:
flyers dina ba su da kyau
DP da bio dina ba su jan hankali
wall link dina ba shi da tsari
Amma ban tsaya ba. Na ci gaba da gyarawa, koyon sabbin abubuwa, da aiwatar da duk abin da na koya.
Na fara WhatsApp ads, daga nan ne kalubale😠😢 s**a fara:
WhatsApp bans akai-akai😓😭
wani lokaci ina tsakiyar class sai Mark Zuckerberg yayi banned number ta.
wani lokaci ina kusa da rufe sale sai a bani ban
wani lokaci ads ya kare babu ko sale guda😓🥹💔
Akwai lokuta da na yi fushi sosai, na ji kamar:
“Wannan business ba nawa ba ne”
“Zan daina”
Amma ban daina ba. Na dage, na yi hakuri, na yi addu’a, na nemi taimakon Allah.
A June ko July, ta hanyar wannan dagewa da aiwatarwa, Allah Ya kai ni matakin certificate na ₦100,000. Wannan ya kara min kwarin gwiwa sosai. Duk da haka, ban tsaya ba — na ci gaba da aiki.
A November2025, na sake kai wani babban mataki, inda na samu certificate🔥❤️ na ₦200,000. Ba nan kawai ba, duk certificate da aka samu yana zuwa da milestone reward na 10% daga valpulse, wanda hakan ya sa na samu bonus reward a kan nasarorin da na cimma.✅🥰
Wani abin da ba zan taba mantawa da shi ba, shi ne ranar Eid El-Fitr(March 2025), kafin mu je sallar idi, inda Allah Ya bani nasarar cin sales challenge na ₦25,000.🙌💥 Wannan rana ta kara tabbatar min da cewa hakuri da dagewa ba su tafi a banza ba.
A wannan tafiya:
na koya affiliate marketing
na koya video editing
na koya graphic design
na koya ads, landing pages, da content creation
na sayi karin courses (har da Amazon KDP)
na fara koyar da wasu, Alhamdulillah🤲🥰🤍
Ko a lokacin da na rasa waya, ban daina ba. Da na samu sabuwa, na ci gaba da abin da na fara.
Darasin da na koya a shekara 1:
Consistency tana doke komai
👉 Aiwatarwa tafi sani✅
👉 Hakuri mabuɗin nasara ne✅
👉 Idan ka daina, ba zaka taba ganin sakamako ba
Da ace na daina a lokacin da abubuwa s**a yi zafi, ba zan kai inda nake a yau ba.
Ina raba wannan ne domin duk wanda yake tunanin daina abunda yasa a gaba yau, ya san cewa:
Duk mai hakuri, Allah Yana tare da shi.
Allah Ya sanya albarka a lamuran mu bk daya 🤲