
11/11/2024
Gwamnan jihar Jigawa ya bada umurnin karisa wasu manyan ayyukan tituna guda 17 da aka fara su tun a gwmanatin da ta gabata.
A yanzu haka Gwamnan yana kan gudanar da ayyukan Tinubu guda 41 masu tsayin kilo mita 839 a fadin jihar Jigawa.
Ga jerin titunan da ya bada umurnin a cigaba da gudanarwa;
1. Gina titin Maigatari-Jobi- Kuka Tankiya-Dan Takore- Danbanki-Dangwanki-Danmakama Mekekiya-Maizuwo-Baruma- Bandakado-Lululu zuwa Unguwar Gawo-Babura.
2. Gina titin Shuwarin-Wurma-Chamo-Abaya-Isari.
3. Gina titin Girimbo-Gantsa Kauya-Sagu-Kwanar YayarinTukur Lelan Kuou-Kukuma-Sara.
4. Gyara lalataccen sashen titin Dutse-Baranda-Waza-Gambara.
5. Gina titin Sule Tankarkar-Amanga-Maitsamiya-Tsugudidi-Santarbi-Garin Alko.
6. Gyara lalataccen sashen titin Birnin kudu-Sundumina zuwa Kiyawa.
7. Gyaran lalataccen sashen titin Jahun zuwa Gujungu.
8. Gina titin Kwanar Kuka- Gasanya-Manaba-Kutugu- Tagadawal-Akurya zuwa Tata.
9. Gina titin Yelleman-Kaugama zuwa Kwanar Madana.
10. Gina titin Auyo - Kaffaddau zuwa Ayama.
11. Gyaran lalataccen sashen titin hanyar Auyo-Kafin Hausa.
12. Gyaran titin Darai- Gilima
13. Gyaran hanyar Hantsu-Miga-Dangyatin
14. Gyaran hanyar Kiyawa-Jahun
15. Gyaran hanyar Kwalam-Gilima-Majiya
16. Gyaran hanya tare da gina kwalbatoci garin Gudunya a kan hanyar kanya Baba-Yarkirya- Babura
17. Gyaran hanyar Birnin Kudu-Zazika.