10/07/2025
DARASI NA 3
TARIHIN HIJIRAR SHEHU USMANU ƊAN FODIYO DA KAFUWAR DAULAR MUSULUNCIYA A (1804)
Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo, babban malami ne, mai gyaran addini, kuma jagoran addini, ya yi fice a cikin tarihin Afirka da Musulunci ta hanyar gwagwarmayar sa da hijirar sa daga Gobir zuwa Gudu a shekara ta 1804
hijira wacce ta zamo ginshiƙi ga kafa Daular Musulunci ta Sokoto. Wannan post din zai bayyana dalilan hijirar Shehu, da yadda aka karɓe shi a Gudu, da yadda aka kafa daular bisa Qur’ani da Sunnah.
A lokacin da Shehu ke yawo yana wa’azi a ƙasar Gobir, sarakuna irin su Sarki Nafata da Sarki Yunfa sun fara tsoron yawan mabiyansa da tasirinsa.
Sun haramta wa almajiransa tafsiri da karantarwa,
S**a hana koyar da mata da yawaita karatu a gida.
Shehu ya tsayawa mata da almajirai yana kare hakkinsu da ‘yancinsu na ilimi. Sai ya yanke shawarar barin ƙasar Gobir saboda rashin damar gudanar da Musulunci yadda yadace.
Shehu tare da danginsa da almajiransa s**a bar Gobir zuwa Gudu, wani ƙauye a arewacin Sokoto a yau.
A Gudu, al’umma s**a taru s**a yiwa Shehu mubaya'a a matsayin Shaykh al-Islam kuma jagoran Musulmi.
Wannan mubaya'a ce ta yarda da jagoranci bisa Shari’a.
Wannan shine tushe na kafa Daular Musulunci ta Sokoto, wacce ta bazu zuwa Kano, Katsina, Adamawa, da wasu sassa na Nijar da Kamaru.
Wannan tarihin yana cikin Littattafan Tarihi da Rubuce-rubucen Shehu da ɗansa Muhammad Bello Sarkin Musulmi
Ga littafafan k**ar haka👇
Na 1. Bayān Wujūb al-Hijrah na Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo
Shehu ya tabbatar da wajibcin hijira daga ƙasar da ake hana addini.
Ya ambaci Suratun Nisa’i aya 97 a matsayin hujja.
Na 2. Wathīqat Gudu (Takardar Gudu)
Takarda da Shehu ya rubuta bayan hijirar Gudu wacce ta ƙayyade tsarin daular Musulunci.
Na 3. Infāq al-Maysūr na Muhammad Bello (ɗan Shehu)
Littafin tarihin da ya rubuta dangane da jihadin mahaifinsa da kafuwar daula.
Na 4. Nāsihatu al-Ummah na Shehu Usmanu
Ya bayyana a nan yadda sarakuna s**a jirkita addini da yadda al’umma s**a dauki bidi’a da al'adu
Hijirar Shehu Usmanu Ɗan Fodiyo ita ce farkon tashin hankali da kawo sauyi a tarihin ƙasar Hausa da Musulunci a yammacin Afirka.
Hujja daga littattafan Shehu da ɗansa Muhammad Bello sun tabbatar da cewa kafa Daular Musulunci ta Sokoto ya samo asali daga ilimi, tsoron Allah, da jagoranci na gaskiya.
Zaku iya neman littattafan kuma kuyi binciken ku