14/10/2025
GIDAN MACE
*Akwai wata magana da ta shahara sosai cewa Mace ba ta da gida nata domin a farkon rayuwarta tana zaune a gidan mahaifinta daga baya a gidan mijinta sannan daga ƙarshe a gidan ’ya’yanta maza*
*Wannan magana tana da daɗin ji, kuma mata da dama suna yawan faɗinta Amma menene gaskiyar lamarin*
*Gaskiyar ita ce ba wani gida da zai zama cikakke ba tare da mace ba Idan ka lura da gidajen da maza kaɗai ke zaune mutane ba sa jin daɗin ziyartarsu ko shiga mu’amala da su*
*To me ke sa ginin bulo da siminti ya zama gida mai ɗauke da soyayya, jin daɗi da dariya*
*Wannan daraja mace ce kawai Allah ya ba ita ita ce ke kawata gida da kulawa soyayya da natsuwa*
*Ko da mace ba ta mallaki gida ba, amma gida nata ne domin gida ba ya cika ba tare da mace ba gida ba zai taɓa zama gida ba idan babu mace a ciki...💯*