14/08/2025                                                                            
                                    
                                                                            
                                            🔐 *Me Ke Haddasa Sace-Sacen Pi?* 🤔
Yawan sace-sacen Pi da ake fama da su a yanzu ba daga cikin *Pi App* ake yinsu ba, *ta hanyar wallet browser ne*! Ga abubuwan da ke haddasa hakan:
1️⃣ *Fitar da Private Key 🔑* – Idan ka baiwa wani private key ɗin ka, an gama! Za a iya kwashe duk Pi ɗinka.
2️⃣ *Fake Websites 🌐* – Wasu suna kirkirar shafukan bogi da suke k**a da wallet na Pi. Idan ka shiga ka saka bayananka, sun kwashe komai.
3️⃣ *Wallet Connect Tricks 🎣* – Wasu suna turo fake links da sunan "Connect Wallet" ko "Claim Bonus", amma ashe izinin shiga wallet ɗinka suke nema.
4️⃣ *Rashin Tabbatar da Link 🔍* – Wasu na shiga wallets daga browser ba tare da sanin ko daga inda link ɗin ya fito ba, hakan ke jefa su cikin haɗari.
📌 *Shawarata*:
✅ Kada ka taɓa bayyana *private key* naka!
✅ Ka riƙa amfani da wallet ɗin Pi daga cikin *official Pi Browser App*.
✅ Guji danna kowanne link da baka tabbatar da ingancinsa ba.
💥 *Pi ba a sacewa kai tsaye* – sai dai idan kai ka buɗe wa masu sata ƙofa! Ka kiyaye lafiya da Pi ɗinka! 💜⚡ 
*Shawara ta 2
Idan kana da Lock Up balance acikin wallet din Ka Wanda kake jiran Kwanakin su ƙare kafin su zama available Ka cire su.
Yana da kyau, ka gwada tura Pi tokens k**ar guda biyu cikin wallet ɗin ka, kabar su na tsawon kwanaki uku, ka gani, idan an cire, ya tabbata wallet din an yi compromising ɗin sa.
Idan kuwa s**a kai wannan kwanaki, so samu ma, su yi sati ɗaya ne. Idan ba a cire su ba, hankalin ka kwance, Lock Up balance din Ka na ƙarewa zaka cire kayan ka.
Akwai kuma, wanda ba a musu migration ba, amma wallet din su yanzu haka yana hannun hackers, ma'ana an yi compromising ɗin sa, zasu sha wahala su yi Mining, har a musu migration, karshe a sace su bayan Lock up ya ƙare.
Hanya ɗaya ne kawai zaka gane, wallet ɗin ka na Pi Kai kaɗai ke da iko da shi koh akasin haka, shine ka sayi Pi biyu ka tura cikin sa kajira ka gani.
Allah ya tsare mana baki daya
Kuma Allah yasa mudace 🤲💪🙏