11/10/2025
Matashin da ya canza rayuwarsa da ilimi, ba da connections ba.”
Akwai wani matashi daga Arewa wanda ya fito daga iyali masu ƙarancin ƙarfi.
Rayuwarsa cike take da ƙalubale – babu aiki, babu tallafi, babu wanda zai tsaya masa. Amma akwai abu guda da yake da shi: burin canza rayuwarsa.
Kullum yana ganin yadda wasu ke samun nasara a internet – daga freelancing, editing, crypto, da digital business.
A maimakon ya ce “ba zan iya ba,” sai ya fara neman ilimi a kan waya. YouTube, Google, da Telegram s**a zama makaranta gare shi.
Yayi ta ƙoƙari, yana fadi yana tashi. Amma yau, wannan matashi ya zama abin koyi – yana koyar da sauran matasa, yana samun kuɗin halal, kuma yana taimaka wa iyayensa.
Wane sirri ne?
Ba wani abu ba ne – ilimi, aiki tukuru, da imani da kansa.
Arewa tana da dubban irin waɗannan matasan — amma da yawa sun tsaya jiran taimako.
A gaskiya, ba sai kana da “connection” ba, sai kana da “conviction.”
Idan kana da wayar Android, kana da internet, to kana da damar da zai iya canza rayuwarka.
Kawai ka fara yau.
Ka fara neman ilimi.
Ka fara koyon digital skills.
Ka fara aiki da niyyar ficewa daga jahilci da talauci.
🗣 Tambaya a ƙarshe:
> A ganinka, me yafi muhimmanci a rayuwar matashi — “connection” ko “direction”?
👇 Ka faɗi ra’ayinka a comments.
✍️ Arewa Youth Tech