
06/08/2025
INNA LILLAHI WA INNA ILLAIHIR RAJU'UN
Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Ikamatus Sunnah na Jihar Kebbi, Sheikh Imam Aliyu Ladda Bunza a madadin Kungiyar na alhinin sanar da ku rasuwar Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bidia Waiqamatis Sunnah na Karamar Hukumar Mulki ta Argungu, Mal. Umar Abubakar Kokoshe.
Wanda Allah SWT yayi ma rasuwa a yau Assabar 12 Saffar, 1447 wanda yayi daidai da 06 Aug, 2025.
Za'ayi Jana'izar sa da Misalin Karfe 10:040am na safe. A cikin Garin Argungu. Gobe Laraba In sha Allah
Allah SWT ya gafarta masa kurakuren sa, ya haska ka kabarin sa, ya sanya albarka a cikin zuriyar sa, Allah SWT ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makoma a gare shi.
Allah ya ba mu hakurin jure wannan Babban rashin da muka yi. Allah ya sa mu cika da Imani Idan ajalin mu ya yazo.
JIBWIS KEBBI