05/06/2026
Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un
A madadin ni kaina da iyalina da daukacin jama'armu, ina mika sakon ta'aziyya ga iyalai da yan uwan Malam Abubakar Sadiq Muhammad (Pharmacy), wanda Allah SWT ya karbi rayuwarsa a safiyar yau bayan fama da jinya.
Malam Sadik Pharmacy jajirtaccen matashi ne wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen karantarwa da kokarin tabbatar da adalci da shugabanci nagari. Rashinsa a wannan lokaci zai haifar da gibi mai wuyar cikewa.
Ina rokon Allah SWT ya jikansa da rahama, ya bashi aljannatul Firdausi, Allah ya bawa iyalai da yan uwa hakuri da dangana