26/08/2022
RANAR HAUSA TA DUNIYA
Su Waye Hausawa?
Daga Al-mansoor Gusau
Hausa al'umma ce dake zaune a Arewa maso yammacin tarayyar Nijeriya da kuma kudu maso yammacin Jamhuriyyar Nijar.
•Al'umma ce mai ɗimbin yawa, sun bazu a cikin ƙasashen Afirka da ƙasashen Larabawa, kuma a al'umma ce mai matukar hazaƙa, aƙalla akwai sama da mutane miliyan hamsin (50) wadanda harshen Hausa shi ne asalin harshen da su ke magana da shi.
•A tarihi ƙabilar Hausawa na tattare a salasalar birane watau alqarya. Hausawa dai sun sami kafa daularsu ne tun daga shekarun 1300's, sa'adda s**a sami nasarori da dauloli k**ar su daular Mali, Songhai, Borno, da kuma Fulani, a karni na 19 Hausawa suna amfani da Doki ne domin yin sifiri da balaguro.
•Mutane kimanin sama da miliyan 50 ne ke magana da harshen Hausa a Najeriya, Nijar, Arewacin Gana da kuma wasu al’umma daga yankin Kaolack a Senigal har zuwa Khartum dake ƙasar sudan, asalin inda zuciyar Hausawa take shi ne garin Kano, Katsina da Sokoto.
•Asalin al’ummar Hausawa maguzawa ne, amma sun shafe daruruwan shekaru da karbar addinin musulunci ƙarƙashin mulkin sarakunan Haɓe, wanda s**a daina yin bori da tsubbace-tsubbace, zuwan Shehu Usman Ɗan Fodio ne yasa ya kawar da mulkin wadannan sarakunan na ƙasar Hausa, ta hanyar yaƙar Hausawa da sarakunansu na haɓe a Gobir, Zazzau da wasu yankunan ƙasar hausa. Wanda wannan juyin mulkin ne yasa Usman Ɗan Fodio ya kafa Daular Fulani a Hausa Fulani a ƙasar Hausa Kuma Hakan yasa masarautun ƙasar Hausa sun kasance a ƙungiyar Tuta ɗaya na Usman Ɗan Fodio.
•Hausawa suna kiran al’adunsu da al’adan gargajiya, wacce su ke yi duk shekara, ko a talabijin ko Bidiyo, ko kuma aikace cikin al’amuran yau da kullum.
•Na daga cikin rubutun Hausawa, suna yin rubutu ne asali da Ajami, rubutu ne da haruffan larabci amman a luggar hausa, kuma suna rubutawa ne a fallen takarda.
Harshen Hausa yana da ire-ire da yawa k**ar haka:
GABACIN HAUSA.
Kanawa
Kataguwa
Hadejawa
Gumelawa
Katsinawa
YAMMACIN HAUSA.
Daurawa.
Sakkwatawa.
Katsinawa.
Kurfayawa.
Gobirawa.
Adarawa.
Kebbawa.
Zamfarawa.
Babu ko shakka harshen Hausa, rayayyen harshe ne da Allah (SWT) ya daukaka kima da darajarsa a duniya, domin kuwa shi kadai ne harshen da ke iya aron haruffan wani harshe ya yi rubutu da shi da harshensa na Hausa, mai asalin harshen ya kasa karanta abunda Bahaushe ya rubuta da haruffansa.
Ajamin Larabci: - Bahaushe ya ari haruffan Larabci ya mayar da su na Hausa, wanda Balarabe ba zai iya karantawa ba, kuma ya tabbatar da haruffansa ne aka juya.
Ajamin Boko: - Haka zalika Bahaushe ya ari haruffan Boko na Ingilishi ya rubuta magana da harshensa na Hausa Bature ba zai iya karantawa ba, dole sai dai kallo ko kuma ya nemi sani a gurin al’ummar Hausawa.
Al’ummar Hausawa ne ko da Addinin Musulunci ya shigo kasarsu ta Hausa ya tarar da su da kyawawan halaye da dabi’un da su ka yi dai-dai da koyarwar Addinin Musulunci, shi ya sa ma Bahaushe ke yi wa kabilun Nijeriya da su ka karbi Addinin Musulunci kallon hadarin kaji:
MISALI:
•Zumunci.
•Kunya.
•Kara.
•Taimako.
•Kyamar zina.
•Kyamar sata.
•Auren mace fiye da daya.
- Kai rabu da shi Musulunci Bayarrabe.
- Kai ai ka san daga baya ya Musulunta.
- Kai ai ka san asalinsu ba Hausawa ba ne.
Muna rokon Allah (SWT) ya cigaba da daukaka kima da darajar al’ummar Hausawa a Nijeriya, Nijar da duniya baki dayanta, Allah (SWT) ya kawo zaman lafiya, kwanciyar hankali, walwaha, arziki a cikin al’ummar Hausawa da Addinin Musulunci, Allah (SWT) ya zaunar da Arewacin Nijeriya da Kudancin Nijar da daukacin kasashen lafiya alfarmar Annabi Muhammad (SAW).
AL’MANSOOR GUSAU,
ADVOCATE.
26 August 2022.