Danfulaniee Creations

Danfulaniee Creations Digital Creator

15/05/2025

Allahumma Salli Alah Muhammad Wa Ahli Muhammad 🌹❤️

The Day of Martyrs – 25th Rajab (A poem by me)On this day of solemn grace,We remember their noble face.Martyrs stood, th...
25/01/2025

The Day of Martyrs – 25th Rajab (A poem by me)

On this day of solemn grace,
We remember their noble face.
Martyrs stood, their hearts ablaze,
In justice’s name, they paved the way.

Chained by tyrants, yet unshaken,
Their oaths to truth were never forsaken.
From fields of struggle to prison’s gloom,
They carried the torch that lights the tomb.

Cries of the oppressed, they bore,
A voice for the silenced, forevermore.
With every step, their souls ascended,
For faith and honor, they defended.

The blood they spilled was not in vain,
It nurtures hope through the pain.
In every tear, their courage gleams,
Alive in hearts, their endless dreams.

O movement pure, O cause divine,
Your martyrs rise, their lives refine.
Though they rest beneath the skies,
Their truth and legacy shall never die.

On Rajab’s 25th, we bow and pray,
For those who chose the righteous way.
Their sacrifice, a guiding light,
Forever shining through the night.

20/01/2025

ME YASA MUKE SABAWA DA WAHALA (2) —Muhammad Jawad MJWannan hauhawan da kudin abubuwa keyi ya sanya yan Nigeria da dama c...
28/10/2024

ME YASA MUKE SABAWA DA WAHALA (2) —Muhammad Jawad MJ

Wannan hauhawan da kudin abubuwa keyi ya sanya yan Nigeria da dama cikin mawuyacin hali. A lokaci guda kuma an maida ita al'ada, karin kudin mai, abinci da abubuwan yau da kullum yajanta wuce gona da iri. Yanzu fa abinda ya rage na jin dadi wa talakan Najeriya, ya koma bai iya sayen komi se abinda ya zama dole. Kuma fa ba an dena karin bane, kullum se an samu kari a farashin kaya. Tambayar anan shine, sai yaushe za a daina wannan kari? Sai randa talaka yaji cewa abin ya ishe shi.

Fetur, babban dalilin da yasa ake wannan haukar kara kudin. Farashin mai ya ninka kisa sau 2-3 a cikin shekara 1. Kudin mota yayi tsada, inda za a kaika kwanaki N500 yanzu se ka bada N1000 ko sama da haka. Yau kayan gona ma tsada suke. Ba fa noman bane matsala, a'a kudin da za a kashe wurin jigilar kayan daga gona zuwa cikin gari shine yayi yawa. Tumatir wannan se kaji ana wai babu na N100. Kuma fa duk sabida farashin mai ne koh? Kuma ance muna da mai a Najeria, to me yasa yake tsada? Sabida mun tara azzalumai a matsayin shuwagabanni.

Abincin da yake na marmari a da, wandq ba a damu ma dashi ba ya zama yadda ya zama yanzu. Shima ya koma yanzu ba kowa ke iya siya ba. Su shinkafar nan, Garin Kwaki, doya, masara duk sun kusa gagarar talakan Najeria, kullum kara kudi suke. Wannan tasa mai siyan Kwano daya ya koma Rabi ko Gwangwani. Abinci ma kenan da ya zama dole a rayuwa ya gagara ina ga kayan more rayuwa.

Suma fa masu karamin jari karba suke yi. Karamin dan kasuwa ya saba siyan abu da arha, amma a wannan halin da ake ciki, ribar kara tsukewa take, kullum an an siyar aka je siya se anyi ciko. Da in ana siyar Kwali 20, yanzu dakyar ake siyan 5. Me ya jawo wannan? Ga bashi yayi yawa malam.

A haka de dan kasa ke cigaba da rayuwa da fatan Alllah ze kawo masa mafita. Ba fata muke ba, amma aka cigaba da tafiya a haka se an kai lokacin da ga kudin amma ba za su isa ka siya abunda kake so ba, sabida yafi karfin abinda kake samu.

Ya kamata a gane fa, a nemi mafita ko don aci abinci.

Zan cigaba insha'Allah...

ME YASA MUKE SABAWA DA WAHALA (1) — Muhd Jawad MJA Najeriyar mu ta yanzu, sabawa da wahala ya bi jikin mutane. A maimako...
25/10/2024

ME YASA MUKE SABAWA DA WAHALA (1) — Muhd Jawad MJ

A Najeriyar mu ta yanzu, sabawa da wahala ya bi jikin mutane. A maimakon a nemi mafita daga halin da ake ciki na tsadar rayuwa, amma kowanne a cikinmu gani yake ai babu wani abun da za a iya yi har ma kaji mutane suna fadin: "To ya za muyi, Allah ya h**e mana abin siya," to tambayar aman itace, ME YASA MUKE SABAWA DA WAHALA".

Daga shekarar 2023 zuwa yanzu da nake wannan rubutun abubuwa nawa ne s**a kara tsada kuma suke cigaba da kara tsada? Mu dauki misalin Shinkafa wacce ta zama abinci ga kusan kowa yanzu, daga farashin #1000 a kowane kwano yanzunta kai kusan #3000, haka sauran abubuwa ma. In wani na iya siya, wani fa?

Abin dubawa anan shine, samu fa baya karuwa. In aikin gwamnati kake yi toh ba wani karin albashi, in dan kasuwa ne kai, in ka siyar toh sai kayi ciko zaka siyo wasu kayan. Haka kuma ake cigaba da tafiya kullum tare da imamin cewa "Allah zai kawo abin siya".

wannan tunanin shi ke sa abubuwa suna kara kwabewa. Se ake ganin ai ba laifin shuwagabanni bane. Haka wannan tunanin shi ke sa a rika tunanin babu mafita kuma a cigaba ta tafiya a haka wanda karshe ba abinda ze kawo sai wahala mara karewa (ba fata muke ba). Ba wanda ya shirya sadukar da jin dadin sa domin samun ingantacciyar rayuwa nan gaba, sai dai kawai anyi imani da cewa wai "No condition is permanent".

Muniya fahimtar cewa wannan sabon shine farkon matsalar. Hakan ze bamu damar fahimtar matsalarmu ba komi bane illa zalunci da kuma tsarin gwamnatin dake tafiyar da kasar.

Zan cigaba insha'Allah....

Address

Abuja

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Danfulaniee Creations posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Share