AREWA MEDIA

AREWA MEDIA Keeping you updated with trending fact.

16/06/2022

Domin sanin halida duniya keciki

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya shawarci masu neman takarar shugabancin ƙasar a jam'iyyar APC su sasanta a tsaka...
05/06/2022

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya shawarci masu neman takarar shugabancin ƙasar a jam'iyyar APC su sasanta a tsakaninsu don amincewa da mutum ɗaya ya wakilci jam'iyyar a zaɓen shugaban ƙasar na 2023.

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya lashe zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyya...
29/05/2022

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya Atiku Abubakar ya lashe zaɓen fitar da gwani na ɗan takarar shugaban ƙasa a jam'iyyar PDP.

Atiku ya lashe zaɓen ne bayan da ya samu ƙuri'a 371. Ya kayar da gwamnan Jihar Rivers Nyesom Wike wanda ya zo na biyu da ƙuri'a 237.

Tsohon shugaban majalisar dattawan Najeriya, kuma shugaban kwamitin ya gudanar da zaben, David Mark, ne ya bayyana sakamakon zaben wanda aka gudanar a Abuja, babban birnin kasar.

A jawabin da ya yi bayan nasarar da ya samu, tsohon mataimakin shugaban kasar ya caccaki gwamnatin APC mai mulkin Najeriya, yana cewa ta ja wa kasar koma-baya, kasancewar babu abin ta yi sai warwarare ayyukan alherin da ya ce jam`iyyarsa ta PDP ta shuka gabannin APC ta yi mata kaye a shekara ta 2015.

Amma ya yi alwashin cewa zai mayar da Najeriya a kan kyakkyawar turba idan ya samu nasarar zama shugaban kasa.

Kafin fara zaɓen ne gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwar ya sanar da janye wa Atiku, tare da umartar magoya bayana su zaɓi Atiku Abubakar.

Ƙuri'ar da kowanne ɗan takara ya samu

Tariela Oliver 1

Sam Ohabunwa 1

Pius Anyim 14

Udom Emmanuel 38

Bala Mohammed 20

Bukola Saraki 70

Nyesom Wike 237

Atiku Abubakar 371

Ayo Fayose 0

Dele Momodu O

Charles Ugwu 0

Chukwendu Kalu 0

Ba wannan ne farau ba

A shekarar 2019 ma Atiku ya yi wa PDP takara, amma ya yi rashin nasara a babban zaɓe, wanda Shugaba Muhammadu Buhari mai ci ya lashe.

Atiku, mai shekara shekaru 75, zai fuskanci duk wanda APC za ta tsayar a nata zaɓen da za ta yi a ranakun shida da bakwai na watan Yuni.

Wannan ne karo na uku da aka zabi Atiku Abubakar don yin takarar shugaban ƙasar Najeriya ba tare da ya samun nasara ba.

Tarihin Atiku Abubakar, mutumin da aka tsayar takarar shugaban Najeriya karo na uku

PDP na gudanar da babban taron fitar da dan takarar shugaban kasa

28/05/2022
28/05/2022

DAGA JARIDAR RFI HAUSAKasar Faransa ta ce zai dauki shekaru 15 zuwa 20 kafin Ukraine ta zama cikakkiyar mamba a cikin ku...
22/05/2022

DAGA JARIDAR RFI HAUSA

Kasar Faransa ta ce zai dauki shekaru 15 zuwa 20 kafin Ukraine ta zama cikakkiyar mamba a cikin kungiyar kasashen Turai, sabanin yadda shugaba Volodymyr Zelensky ke bukata cikin gaggawa.

DAGA JARIDAR RFI HAUSAWasu ‘yan bindiga a Najeriya sun fille kan Okechukwu Okoye, dan majalisa mai wakiltar al’ummar Gwa...
22/05/2022

DAGA JARIDAR RFI HAUSA

Wasu ‘yan bindiga a Najeriya sun fille kan Okechukwu Okoye, dan majalisa mai wakiltar al’ummar Gwamna Charles Soludo a majalisar dokokin Anambra da ke yankin Kudu-maso-gabashin kasar.

DAGA JARIDAR DW HAUSATELBIJIN KAI TSAYEBATUTUWALABARAIRasha ta katse sayar wa Finland da Iskar GasDaga Muntaqa Ahiwa |...
22/05/2022

DAGA JARIDAR DW HAUSA

TELBIJIN KAI TSAYE



BATUTUWA

LABARAI

Rasha ta katse sayar wa Finland da Iskar Gas

Daga Muntaqa Ahiwa | awa 23 da ta wuce



A wani sabon salon tsama ta diflomasiyya, hukumomi aFinland sun bayyana cewa Rasha ta katse samar da iskar gas da take sai da wa kasar. Matakin ya shafi har da Estonia.

Kamfanin da ke hada-hadar gas a Finland wato Gasum, ya tabbatar da katsewar makamashin wanda ke bi ta bututun da ya ratsa kasashen yankin Baltic da ya hada da Finland din da ma kasar Estonia.

Tun da fari dai kamfanin na Gasum ya ki amincewa ne da ya batun ci gaba da biyan kudin iskar ta gas da kudin kasar Rasha wato Ruble.

Matakin katse cinikayyar makamashin ya zo ne daidai lokacin da kasar Finland ke gab da shiga kungiyar tsaro ta NATO.

Finland din dai ta kuduri aniyar shiga kungiyar ne, bayan mamayar da Rasha ta yi wa kasar Ukraine.

KANUN LABARI DAGA DW HAUSAMasana sun sanar da yadda aka samu karin mutane biyu da s**a kamu da kyandar biri a yayin da a...
22/05/2022

KANUN LABARI DAGA DW HAUSA

Masana sun sanar da yadda aka samu karin mutane biyu da s**a kamu da kyandar biri a yayin da aka soma baiyana fargabar cutar ka iya zama wata annoba a duniya.

Address

Azare

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when AREWA MEDIA posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to AREWA MEDIA:

Share