16/10/2025
Yadda ake trading da Bollinger Bands (BB).
🎓 Ana amfani da Bollinger Bands a ranging ko consolidating market.
Hanyoyi biyu (2) da muke trading na BB:
1. Bollinger Bounce.
2. Contraction and expansion.
Bari muyi bayani da 4H timeframe:
✅ Bollinger Bounce: Idan kasuwa ya daki lower band, har Candlestick ya ɗan leko kansa waje.
Wannan na nuna oversold.
Sai ka nemi reversal pattern kamar hammer ko engulfing.
Target 🎯: TP1 Middle band/line, TP2 upper band.
Confirmation 👍: RSI oversold (reading ɗinka 1-30).
====================================
✅ Contraction/squeeze and expansion: Idan bands ɗinka s**a matse, wannan shi ne contraction.
Bayan contraction/squeeze ana jiran expansion.
Expansion yana iya faruwa ta sama ko kasa.
🎖️ Entry: Idan candle ya buɗe daga cikin band, sannan ya je yayi closing a wajen upper band.
Confirmation 👍: Ka jira next Candlestick, ya buɗe, kuma ya rufe a wajen upper band.
Sai ka shiga a open na next Candlestick.
Exit: idan kasuwa ta dawo ta taɓa middle line.
A takaice waɗannan sune hanyoyi biyu (2) da traders ke amfani da Bollinger Bands.
Ana iya amfani da RSI ko MACD wajen karfafa signal na Bollinger bounce.