26/11/2025
Dalilin da yasa na ce kowa yana bukatar aje baking soda.
Baking soda da baking powder suna kamaiceceniya amma ba abu daya ba ne, baking soda zallar sodium bicarbonate ne sabanin baking powder dake dauke da starch da acids like tartaric
Baking Soda iri abubuwan nan ne (kamar su gishiri da ba a son rasa su a gida saboda amfaninsu)
Ga kadan daga cikin amfaninsu
Wajen girki
1 Yana daga fulawa kamar baking powder
2 Yana rage tsamin miya
3 Yana saka wake ya dahu da wuri (Za ku rage asarar gaushi da gas๐ซฐ)
4 Ana yin girke girke kala kala da shi
Amfanin cikin gida.
1 Ana wanke tiles, toilet da sauransu
2 Yana iya cire dattin da ya makale a riga ko carpet
3 idan fridge, takalmi, ko dustbin dinki ya yi wari kina iya barbada bakin soda
4 Idan rariyarki ta toshe ki hada shi da vinegar a ruwan zafi zai bude
5 Ana wanke silver, samira, tukunya, plastics plate da sauransu za ki ga sin yi kalkal
Amfanin jiki
1 Ana brush da shi (yana saka hakori haske)
2 Ana shafawa a hamata yana cire wari, mqza ga tips๐
3 Ana cika shi a ruwa a saka kafa yana rage warin kafa
4 Ana wanke gashi da shi yana cire dattin da s**a makale a scalp
Amfani saboda lafiya
1 idan zuciyarki na zafi kina iya cikawa ki sha
2 idan cinnaka ko sauronya cije danki kima iya shafa masa a wajen
3 Ana iya kurkurar baki yana rage warin baki
Amfani a gona
1 Yana gyara kasar da acid ya mata yawa
2 Yana kashe kwari
A skincare
1 Ana iya rage Ph (masu formulation)
2 Wasu na scrub da shi (amma scrub dinsa yana irritating saboda matsalar pH don haka a kiyaye)
Nan fa wai kadan daga amfaninsa na lissafo, to yanzu don Allah wannan abin bai cancanci a ce yana nan a gidan kowa ba??? Da 500-1k din ki zali samu gwangwaninsa a wajen masu sayar da kayan girki ko kayan cake, ko supermarket.
So duk wadda ya karu da sabon abu kar yayi bakin ciki a yan uwansa ya yi share ko mentioning din wasu su karu