14/09/2025
Yadda Za Ka Samu Lambar Haraji (TIN) Kafin Wa’adin Janairu 2026 Ga Masu Asusun Banki
Idan kana da asusun banki a Najeriya, daga farkon shekarar 2026 za a bukaci ka samu Lambar Shaidar Haraji (TIN) domin ci gaba da amfani da asusunka. Wannan sabuwar doka tana fara aiki ne daga 1 ga Janairu, 2026, bisa tsarin Dokar Gudanar da Haraji ta Najeriya, 2025. Wannan babban sauyi ne a harkar haraji a ƙasar, wanda zai shafi duk wanda ke da asusun banki.
Sai dai kuma, samun TIN a yanzu abu ne mai sauƙi kuma kyauta gaba ɗaya. A mafi yawan lokuta, an riga an ƙirƙiro maka TIN ta hanyar Bank Verification Number (BVN) ɗinka ko kuma National Identification Number (NIN) ɗinka.
Matakan Da Ake Bi Don Samun Lambar Haraji (TIN)
An tsara wannan matakan cikin sauƙi domin kowa ya iya bin doka ba tare da wata wahala ba.
Mataki na 1: Duba ko kana da Lambar Haraji (TIN) tuni
Ka ziyarci shafin hukuma na Joint Tax Board (JTB) TIN Verification Portal a https://tin.jtb.gov.ng.
Ka danna zabin “Search for TIN”.
Shigar da BVN ɗinka da ranar haihuwarka domin a bincika ko an riga an ba ka TIN ta atomatik.
Mataki na 2: Yi rijistar sabon TIN (idan ba ka da shi)
Idan bincikenka bai nuna maka TIN ba, sai ka yi rijista sabuwa.
Ka shiga JTB TIN Registration Portal ta hanyar wannan mahaɗin.
Ka zaɓi “Register for TIN” ga mutum ɗaya.
Cika bayanan da ake buƙata, ciki har da BVN, NIN, da sauran bayanan ka na sirri.
Aika fom ɗin, sannan ka bi umarnin da aka bayar don samun takardar shaidar TIN.
Wannan tsarin gaba ɗaya kyauta ne. Za ka iya sauke takardar shaidar TIN ɗinka daga shafin kuma ka buga ta idan an fitar maka. Ana ba da shawarar sosai ka kammala wannan tsari kafin wa’adin Janairu 2026, domin kada a katse maka damar amfani da asusun banki da sauran ayyukan kuɗi.
Ina fatan Allah Ya rufa mana asiri.
©Umar Usman