09/12/2025
TIN, wanda ke nufin Tax Identification Number (Lambar Shaida ta Haraji), wata lambar ce ta musamman da take zama ginshikin duk wani al'amari da ya shafi haraji da mu'amalolin kasuwanci a Najeriya. Ana ba da wannan lambar ga kowane mai biyan haraji, ko shi mutum ne ko kamfani, ta hanyar hukumar haraji ta ƙasa (FIRS) ko ta jiha.
Muhimmancin samun TIN ba wai kawai don biyan haraji bane, a'a, yana shimfiɗa hanya ce domin samun damar gudanar da wasu ayyukan gwamnati da na kasuwanci masu mahimmanci. Alal misali, bankuna suna buƙatar TIN kafin su bude asusun kasuwanci (Corporate Account) domin tabbatar da cewa kasuwancin ya yi rajista kuma yana bin dokokin haraji. Haka kuma, duk wani mutum ko kamfani da yake da niyyar shiga kwangilar gwamnati, ko neman izinin mallakar ƙasa (Land Registration), dole ne ya gabatar da TIN dinsa. Wannan lambar tana taimakawa wajen tabbatar da ingancin kamfani ko mutum a idon gwamnati da kuma abokan ciniki, wanda hakan ke ƙara amana.
A wani ɓangaren kuma, rashin samun wannan lambar mai muhimmanci yana tattare da matsaloli masu yawa. Na farko kuma mafi mahimmanci, yana iya jawo hukunci da tarar kuɗi mai yawa daga hukumar haraji, wanda hakan zai iya shafan tattalin arzikin mutum ko kasuwanci. Bugu da ƙari, za a hana mai shi duk wata mu'amala da gwamnati da kuma samun damar gudanar da wasu manyan ayyukan kasuwanci kamar fitarwa da shigo da kaya. A takaice dai, rashin TIN zai iya sanya kasuwancin ya zama marar inganci a idon doka, kuma hakan zai takura masa damar bunƙasa da samun nasara. Saboda haka, samun TIN number ba zabi bane, a'a, wajibi ne ga duk wanda yake so ya gudanar da kasuwanci cikin bin doka a Najeriya.