16/09/2025
INNA LILLAHI WA INNA ILLAIHIR RAJU'UN
Shugaban Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Ikamatus Sunnah na Jihar Katsina, kuma Daraktan Da'awah na Kasa, Sheikh (Dr.) Yakubu Musa Hassan Katsina (Sautus Sunnah) a madadin Kungiyar cikin alhini yana sanar da rasuwar Daraktan Agaji na Jihar Katsina Alhaji Abdullahi I.N Bakori
Wanda Allah SWT yayi ma rasuwa a yau 23 Rabi'u Awwal, 1447 wanda yayi daidai da 16 September, 2025 bayan yayi jinya
Za'a sanar da lokacin janadarshi idan an tsaida lokaci
Muna rokon Allah SWT ya jikanshi, ya gafarta ma shi, ya haska ka kabarin shi, ya sanya albarka a cikin zuriyarsa, Allah SWT ya sanya Aljannar Firdausi ta zama makoma a gare shi
Allah ya ba mu hakurin jure wannan Babban rashin da muka yi. Allah ya sa mu cika da Imani idan ajalin mu ya yazo.
JIBWIS Katsina
23 Rabi'u Awwal, 1447
16 September, 2025