29/08/2024
Mu rinka yi wa junanmu kyakkyawar addu`a, domin wanda ya yi wa dan uwansa musulmi kyakkyawar addu`a, shi ma alkhairin da ya roka masa zai riske shi.
Addu`a ita ce takobin mumini, tana tare mana bala`an da suke doso mu, tana rage mana damuwarmu, tana kusantar da mu zuwa ga ubangijinmu.
Ka gabatar da bukatunka zuwa ga ubangijinka, shine zai amsa maka, ba kuma zai yi maka koro ba, sabanin dan adam, da zai kosa da kai, watakila ma ya rinka guje maka.
`Yan uwa ku kasance masu yawaita addu`a, hakan zai yaye mana kuncin rayuwar da muke fama da shi, yau da kullum.
Shawara ce wannan kyauta !
Bintu Abdurrahman ✍🏻