09/11/2025
MURNAR CIKA SHEKARU 4 DA FARA HIDIMA WA AL'UMMA.
Gidauniyar C.I.M Foundation tayi bikin cika shekaru Huɗu da kafuwa. Inda mambobin Kungiyar s**ayi bitar nasarorin da s**a cimma wa tsawon shekaru 4 da kafa Gidauniyar ta C.I.M.
Yayin taron bikin, shugabannin kungiyoyin cigaban gari, Kungiyar Malamai da Ɗalibai na daga cikin nau'in mahalarta taron inda mambobin Gidauniyar C.I.M s**a bayyana salon tafi da lamuran Gidauniyar matsayin faɗaɗa salon shugabanci da dabarun ɗorewar ayyukan kungiyoyin idan s**ayi kwaikwayo ta C.I.M.
Na daga cikin muhimman nasarorin da C.I.M ta samu shine:
1. Ɗaukar nauyin karatu na yara marasa galihu kimanin ɗalibi 12 a makarantun firamare ukku dake karamar hukumar Batsari.(Ɗan waire,Model da Leƙo).
2. Sai horar da yara kimanin 7 sana'o'i domin dogaro da kawunan su tareda basu jari daidai kasuwancin nasu.
3.Biyan kuɗin makaranta ga wasu ɗaliban makarantun gaba da Sakandire da suke shekarar ƙarshe a karatun su.
4.Bada gudunmawa a duk ayyukan cigaban gari a Batsari musamman waɗanda aka gayyaci C.I.M Foundation.
Muna matukar godiya ga mahalarta taron musamman shugabannin kungiyoyi da s**a iya ware mana lokacin su na yau don tayamu murna,Allah hutar da gajiya ya ƙara taimaka mana.