
23/07/2025
Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed a yau ya halarci babban taron tuntuba na shugabannin farko na jam’iyyar PDP da masu ruwa da tsaki na jam’iyyar PDP da aka gudanar a dakin taro na NAF da ke Abuja.
Taron mai taken “Tunawa da farkon, farfaɗo da haɗin gwiwar Mu,” taron ya kasance wata kafa da shugabannin jam’iyyar za su yi tunani a kan tafiyar da jam'iyyar PDP, da tabbatar da muhimman ginshikin da aka kafa jam'iyyar da kuma tsara hanyoyin da za ta bi a nan gaba.
Taron ya tattaro jiga-jigan dattawan jam’iyyar da ake mutuntawa, masu rike da mukamai, da tsaffin shugabanni, inda s**a kara jaddada muhimmancin taron wajen tsara makomar jam’iyyar PDP.
Da yake gabatar da jawabin bude taron, dattijon ƙasa Farfesa Jerry Gana ya ƙalubalanci mahalarta taron da su tuno irin juriya, sadaukarwa, da hangen nesa da s**a haifar da jam’iyyar.
Ya nanata cewa duk da yunƙurin kawo rikicin siyasa na cikin gida na tsawon shekaru, PDP ta kasance babbar cibiya a fagen dimokuradiyyar Najeriya.
A nasa jawabin, Gwamna Bala Mohammed ya jaddada kudirinsa na cigaba da kasancewa a jam’iyyar PDP, ya kuma yaba da irin nasarorin da ta samu.
Sai dai Ya amince da dimbin kalubalen da jam’iyyar ta fuskanta amma ya yaba da juriya da kuma cigaba da ta samu.
Gwamna Bala ya kuma bayyana irin nasarorin da aka samu a jihohin da PDP ke mulki, inda ya bayyana cewa irin ci gaban da aka samu, da samar da ababen more rayuwa, da gudanar da harkokin mulki a wadannan jihohi ya zama ma’auni da sauran jam’iyyu ke kokawa a kai.