14/05/2026
Idan kaga Namiji yana murmushi, yana gaisawa da mutane cikin nishadi, kada ka dauka rayuwar ta yi masa dadi ne.
A'a, Jarumta ce kawai irin ta 'Da Namiji.
Akwai abubuwa 3 da Maza suke boyewa wanda Allah kadai Ya sani:
1. Aljihun Baya:
Zai fita da safe, aljihunsa β¦0.00, amma zai yi shiga mai kyau, ya sa turare. Ba don yana da kudi ba, sai don Kada a raina shi, kuma kada a tausaya masa. Namiji ya gwammace ya ci kasa da ya zama abin tausayi.
2. Kukan Zuciya:
Ana ganin kamar bashi da damuwa, amma yana da lissafin bashi, lissafin kudin hayar gida, lissafin maganin iyaye, da lissafin makomar rayuwarsa. Yana hadiye kukan ne saboda ya san Idan ya karye, gidan gaba daya ya karye.
3. Addu'ar Boye:
A duk sujjadar da ka gan shi yana yi, baya rokon mota ko gida mai kyau tukunna... Yana rokon: "Ya Allah kada Ka bari in wulakanta a idon wadanda suke ganin girmata."
SAKO ZUWA GA DUNIYA:
Kada ku kalli murmushinmu ku ce muna da shi.
Muna murmushi ne saboda mun yarda cewa Mai Bayarwa (Allah) yana sane da mu, kuma Lokaci ne kawai.
Ya Allah, duk Namijin da ya killace damuwarsa a ransa don kada ya dame kowa, yana fafutukar kare mutuncinsa...
Ya Allah Ka kawo masa dauki ta inda ba ya zato, Ka canza masa wannan damuwar zuwa Farin Ciki.
Kuyi sharing idan ku gamsu kuyi farinci da ganin wannan Addu'a.