
15/09/2025
Gwamnatin Tarayya Zata cigaba da shirin ciyar Ciyar Da Daliban Pramary sannan za'a ninka shirin zuwa Dalibai Miliyan 50 a 2026 – Adebowale
__________
A Nijeriya Gwamnatin Tarayya ta bayyana shirinta na faɗaɗa shirin ciyar da dalibai na kasa (NHGSFP) domin ya ƙunshi kimanin daliban makarantar firamare miliyan 50 a shekarar 2026.
Manajan Shirin Kasa na Hukumar National Social Investment Programme Agency (NSIPA), Dr. Aderemi Adebowale, ta bayyana hakan a wata hira da ta yi da Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Abuja.
Ta ce shirin zai haɗa dukkan matakai na farko daga Primary 1 zuwa Primary 6, tare da shigar da yara da ba sa halartar makaranta, a matakin aiwatarwa cikin hankali da tsari.
Adebowale ta kara da cewa:
> “Nan da shekarar 2026, muna sa ran ciyar da kimanin dalibai miliyan 50 a makarantar firamare a Najeriya. A asali, kudin ciyarwa ya kamata ya kasance tsakanin N500 zuwa N1,000 ga kowanne yaro. Ko da akan N500 ga yaro ɗaya, za a iya samar da abinci mai gina jiki kuma mai daɗi a kullum.”
Ta bayyana cewa gwamnati na da niyyar tabbatar da cewa shirin zai taimaka wajen inganta lafiyar yara da kuma karfafa sha’awar zuwa makaranta. Yanda zasu ke samun abinci da zai ishe su a yini kuma mai kyau
Me zaku ce kan hakan.....?