Hamisum GSM repairs & Business Enterprises

Hamisum GSM repairs & Business Enterprises Thank you for contacting GSM Repairs & Business Enterprises.!

Please let me know how can i help you, Dawayarka/kina iya koyan sana arda ka iyafiddakai/ke daka matsalar kudi dasamun biyan bukatun yau da kullum, yi amfanida wayarkadan kasuwanci ta online ✅

12/05/2025

TUNA TARWA ZUWA GA AL'UMMAR MUSULMI: KALLON FINA-FINAN BATSA (BLUE FILMS).

Idan ka Karanta ka Turawa Sauran Ƴan Uwa Domin Su Amfana.

BLue FiLms Fina-finai ne da Wasu Tsageru Daga Cikin Yahudawa Suke Shiryarwa Wanda Yana da ILLa Sosai.

Domin Yanzu Anyi IttiQakin Cewa Ba Abin da Yake Saurin Rufta Mutum Zuwa Zinace-zinace Kamar Shi KaLLon BLue FiLms Ɗin Wanda Zamani Yazo da shi, Ba Ga Namiji ba, Ba Kuma Ga Mace ba.

Babban Abin Takaici Yanzu Yan Mata Sunfi Kowa Qwarewa Wajen Iya KaLLon Wnnn LaLaci na BLue FiLms.

HUKUNCIN SA:

KaLLon Tsaraici Haramun Neh a Shari'ar MusuLunci in Banda Na Matarka Ko Na Mijin ki, BaLLantana Kuma KaLLon Saduwa Tsakanin Mazinata, Wnnn Abune Mai MatuQar Muni Sosai.

Allah Yana Cewa:

"Ka Gayawa Muminai Maza su Rintse Idanuwansu Daga KaLLon Haram Kuma Su Kiyaye Daga Yin Zina".

'Yan Uwa Mu Kiyaye, Duk Wanda Yake KaLLon Irin Waɗannan Abubuwan to LaLLai Yayiwa ALLAH Tawaye.

A Wani Gurin ALLAH Yana Cewa:

"Kada Ku Kusanci Zina hakika ita Zina ALfasha Ce Kuma Mummunar Hanya ce".

Kunga Saboda HaLakan da Take Cikin Zina, Sai ALLAH Yace Kada Mu Kusanceta, shi Kuwa Irin Wnnn KaLLon Yakan Sanya Masu Yinsa su Afka Cikin Zina Kai Tsaye.

Manzon Allah (S.A.W) Yana Cewa:

" ALLAH ka Tsinewa Mai kallon Tsaraici da Kuma Wanda Ake KaLLon Tsaraicin nasa".

Daga Qarshe Ina Qara Jawo HankaLin Masu Yi su Tuba su Daina.....!!!
Don ALLAH Daure ka Rubuta Ameen Bamusan tawa Za'a Karɓa Ba...

Sannan KaLLon Fina-finan Batsa Yana Kai Mutum Zuwa ga Aikata Mummunar Ɗabi'ar Nan ta Istim'na'i Wacce Itama Tana da iLLoLi Ga Lafiya.

Ya ALLAH Ka Tsarkake Mana Zukatan Mu, Ka Kare Zuri'ar Mu Daga Afkawa Cikin Mummunar BaLa'in Dake Tattare Da KaLLon BLue FiLms.🙏🙏🙏

ALLAH Ya Qara Shiryar da Mu da ƴan Uwan mu Masu Aikatawa 🤲.

Kana Son Duba Sahihan Labarai Shigo Jaridar 👉 Wakiliya 👈 Yanzu Yi Following Karku Bari Komai Ya Wuceku...

12/05/2025
11/05/2025
05/05/2025
SHAIƊAN YA NEMI TAIMAKON ALLAH AKAN YADDA ZAI ƁATAR DA ƳAƳAN ADAMU (AS).An karɓo daga Jabir bin Abdullahi (RA) ya ce:"Ha...
03/05/2025

SHAIƊAN YA NEMI TAIMAKON ALLAH AKAN YADDA ZAI ƁATAR DA ƳAƳAN ADAMU (AS).

An karɓo daga Jabir bin Abdullahi (RA) ya ce:
"Haƙiƙa lokacin da Allah Maɗaukakin Sarki Ya saukar da Annabi Adam (AS) zuwa duniya, ya sauka a Indiya. Kuma kan Annabi Adam (AS) yana taɓo sama saboda tsawonsa. Saiƙasa ta koka zuwa ga Ubangijinta saboda nauyin Annabi Adam (AS), sai Allah mai girma da ɗaukaka Ya sanya hannunsa a kan kansa, hakan ya sa ya ragu da zira'i saba’in (70) daga tsawonsa.

Annabi Adam (AS) ya sauko a tare da shi akwai ’ya’yan itatuwa k**ar 'ajwa (irin dabino), utrunj (irin lemo), da ayaba.

Lokacin da aka saukar da shi, sai ya ce: "Ya Ubangijina, wannan bawan na Ka (Iblis) da ka sanya ƙiyayya da gaba a tsakanina da shi – idan ba Ka taimake ni a kansa ba, ba zan iya da shi ba."

Sai Allah ya ce: "Ba za a haifa maka ɗa ba, sai na sanya Mala’ika da zai kula da shi."

Sai Annabi Adam (AS) Ya ce: "Ya Ubangijina, ƙara min."

Sai Allah Ya ce: "Wanda yai kyakkyawan aiki zan saka da mummuna daidai da mummuna, amma kyakkyawan aiki zan ninka ladansa sau goma ko fiye da haka bisa iko na."

Sai Annabi Adam (AS) ya sake cewa: "Ya Ubangijina, ƙara min."
Sai Allah ya ce: "Ƙofar tuba za ta kasance a buɗe har sai rai ya fita daga jikin mutum."

Sa’an nan Iblis ya ce: "Ya Ubangijina, wannan bawanKa da Ka girmama – idan ba Ka taimake ni akansa ba, ba zan iya da shi ba."

Sai Allah ya ce: "Duk lokacin da aka haifa masa yaro, sai a haifa maka naka yaron kai ma."

Sai Iblis ya ce: "Ya Ubangijina, ƙara min."

Sai Allah ya ce: "Zan ba ka damar yawo a jikin ɗan Adam k**ar yadda jini ke gudana, kuma za ka gina gidaje a cikin zukatansu."

Sai Iblis ya sake cewa: "Ya Ubangijina, ƙara min."

Sai Allah ya ce: "Ka kai musu farmaki da dokinka da ƙafafunka, ka kuma sami kaso a cikin dukiyoyinsu da ‘ya’yansu."

An karɓo Daga Aliyu dan Hussain (RA) ya ce: "Manzon Allah (SAW) ya ce: "Lallai ne Shaiɗan yana yawo a jikin ɗan Adam k**ar yadda jini ke gudana."

“Rigar So” – A cikin unguwar Dorayi, birnin Kano, akwai wani matashi mai suna Anas. Shi mai sana’ar ɗinki ne, sananne wa...
03/05/2025

“Rigar So” – A cikin unguwar Dorayi, birnin Kano, akwai wani matashi mai suna Anas. Shi mai sana’ar ɗinki ne, sananne wajen ɗinki riguna masu kyau. Rana guda wata kyakkyawar budurwa ta shigo shagon Anas, tana riƙe da zane.

“Assalamu Alaikum,” ta faɗa cikin murya mai daɗi.
“Wa alaikumus salam, Hajiya,” Anas ya amsa, yana kallon ta cike da nutsuwa.

Sunanta Nafisa. Ta zo ɗinkin riga domin ɗaurin aure na yayarta. Amma a lokacin da Anas ke ɗaukar ma’auni, zuciyarsa ta kamu da ƙaunar Nafisa. Duk da haka bai iya faɗa mata ba. Duk lokacin da ta dawo, sai zuciyarsa ta karye.

A karshe, lokacin da ta zo ɗaukar rigarta, sai Anas ya ciro wata ƙaramar takarda ya tura cikin aljihun rigar. A ciki ya rubuta:

> “Idan kin ji daɗin yadda na ɗinka, to ki ba ni dama na ɗinke zuciyarki da tawa har abada.”

Nafisa ta samu saƙon, ta karanta, sannan ta dawo da murmushi.
“Wannan ɗinkin ka ya k**a sosai… k**ar yadda kalamanka s**a k**a zuciyata.”

Bayan wata guda da auren yayarta, Nafisa ta fara zuwan shagon Anas ba tare da wani dalili mai nauyi ba. Wani lokacin sai ta ce tana so ya gyara mata rigar da ba ta da matsala. A hakikanin gaskiya, zuciyarta na ƙara shanƙwaba da Anas.

Anas kuwa ya mayar da shagon ɗinki tamkar mafarkin zuciyarsa — yana gyarawa da nishadi, yana jira shigowarta.

Wata rana, yayin da suke hira bayan ɗinkin rigar wata kawarta, Anas ya ce:

"Nafisa, ban taɓa jin k**ar ina da abinda zai sa zuciyata ta huce k**ar ke ba."

Nafisa ta sosa kai, tana murmushi:
"Ni ma haka nake ji… Amma baka tambayi iyayena ba tukuna."

Anas ya yi shiru. Daga nan ya fara tattara tsoro da ƙarfin hali ya kai wa mahaifin Nafisa ziyara da niyyar neman izini.

Sai dai... mahaifinta Malam Umar, tsohon malam ne mai tsauri. Ya ce:

"Anas, kai ɗan sana’a ne, kana ɗinki — wannan ba wani abu bane a idona. Amma zan tambayi Nafisa idan ta yarda da kai, ni ba zan hana ba."

Sai aka kira Nafisa gaban kowa. Kunya ta lullube ta, amma ta ce:

"Na yarda da shi, Abba. Yana da gaskiya da mutunci."

Kowa ya yi shi

Address

Toro
Bauchi
122

Telephone

+2348135575860

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Hamisum GSM repairs & Business Enterprises posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Hamisum GSM repairs & Business Enterprises:

Share