Muryar Al'umma TV

Muryar Al'umma TV Media and news

02/08/2026

Fagen Wasanni Tare Da couch fataye Shola...

MEYASA AKE DANGANTA ARZIKI DA ƘWAREWA? Tattaunawa Kan Basirar Fasaha Da Ake Alaƙantawa Da Farfesa Isa Ali PantamiWani ru...
02/08/2026

MEYASA AKE DANGANTA ARZIKI DA ƘWAREWA? Tattaunawa Kan Basirar Fasaha Da Ake Alaƙantawa Da Farfesa Isa Ali Pantami

Wani rubutu da ke yawo a kafafen sada zumunta ya sake jawo muhawara kan irin ƙwarewar fasaha da ake dangantawa da tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arzikin Zamani na Nijeriya, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami.

A cewar masu wannan ra'ayi, ƙwarewa a fannonin Cybersecurity, Artificial Intelligence (AI) da Technology Consulting na daga cikin sana'o'in da ake biyan mafi girman albashi a duniya, musamman a manyan kamfanonin fasaha irin su Google, Microsoft, Amazon da Binance.

Masana harkar fasaha sun bayyana cewa mukaman Chief Information Security Officer (CISO) da AI Research Scientist na daga cikin manyan ayyukan da ake ba su albashi mai tsoka, baya ga ƙarin alawus da wasu fa'idodin kamfanoni.

Rahoton ya kuma yi nuni da cewa idan mutum ya kai matakin ƙwarewar da manyan kamfanonin duniya ke buƙata, samun manyan kuɗaɗe daga ayyukan fasaha, bincike, ba da shawarwari da sauran ayyukan ƙwarewa ba abin mamaki ba ne.

Masu sharhi sun ce a wannan zamani na Knowledge Economy, ilmi, ƙwarewa da gogewa sun zama muhimman kadarori da ke samar wa mutane manyan damar samun kuɗaɗe da tasiri a matakin ƙasa da ƙasa.

Sai dai, ya kamata a lura cewa duk wani iƙirari da ya shafi albashi, dukiya ko kasuwancin kowane mutum yana buƙatar sahihan hujjoji daga tushe mai inganci kafin a tabbatar da shi.



Majiyar Rahoto: Abbah.
— MURYA AL'UMMA TV

02/08/2026

Kabiru Dagash yayi kira ga al'ummar jahar bauchi musamman matasa dasuyi tafiyan APM mai alaman rogo...

02/08/2026

Wannan Goalkeeper Mai Zakuce Akansa ?

Wikki Tourists FC Tayi Kunnen Doki Da Kungaiyar Crown FC A Wasan Sharen Fage...
02/08/2026

Wikki Tourists FC Tayi Kunnen Doki Da Kungaiyar Crown FC A Wasan Sharen Fage...

DA DUMI DUMINTA: Yadda yan wasan Barcelona s**a nuna ƙaunarsu ga Marcus Rashford bayan ya sanar da cewa bazai cigaba da ...
02/08/2026

DA DUMI DUMINTA: Yadda yan wasan Barcelona s**a nuna ƙaunarsu ga Marcus Rashford bayan ya sanar da cewa bazai cigaba da zama a Barcelona a kakar wasa mai zuwa ba.

Yanzu Rashford ya koma Manchester United, inda zai fara shirye-shiryen tunkarar sabon kakar wasa mai zuwa🤝

Abune mai cike da mutuntaka da kuma taɓa zuciya. 🥹

Innalillahi wa’innaillahir rajun Allah ya yiwa Koşan waka Rasuwa Allah ya jikan shi Allah yayi mai rahama Allah yasa alj...
02/08/2026

Innalillahi wa’innaillahir rajun Allah ya yiwa Koşan waka Rasuwa Allah ya jikan shi Allah yayi mai rahama Allah yasa aljanna makoma muma Allah ya kyautata namu zuwan

DA DUMI DUMINTA: Hukumar Shirya Gasar Firimiya ta Najeriya (NPFL) zata gudanar da Babban Taron Shekara-shekara (AGM) a r...
02/08/2026

DA DUMI DUMINTA: Hukumar Shirya Gasar Firimiya ta Najeriya (NPFL) zata gudanar da Babban Taron Shekara-shekara (AGM) a ranar Jumma'a, 7 ga Agustan 2026, a birnin Ibadan, Jihar Oyo.

Bayan kammala taron, za'a gudanar da fitar da jadawalin wasanni (fixtures) da kuma rabon wasannin kakar 2026/2027 ta NPFL a hukumance.

Anasa ran masu mallakar ƙungiyoyi, mambobin kwamitin gudanarwa da sauran masu ruwa da tsaki za su halarci taron domin tsara shirye-shiryen sabuwar kakar wasa.

Muryar Al'umma TV

Kawun 'yan daban fina-finan Indiya 😆(Jarumi Jaya Prakash Reddy)• Asalinsa Kwansutabil ne (Police Constable)• Ya iya wasa...
02/08/2026

Kawun 'yan daban fina-finan Indiya 😆
(Jarumi Jaya Prakash Reddy)

• Asalinsa Kwansutabil ne (Police Constable)
• Ya iya wasa da murya da kwaikwayon muryoyi
• Tun 1988 ya fara fim
• Ya fara ne da kwamedi daga baya ya dawo Boss
• Ya sauya salon muguntar boss a fina-finan Telugu
• Ya kawo salon barkwanci da raha a Bosanci
• Ya kasance marubucin labarai sosai
• Ya shiga siyasa amma bai mayar da hankali ba
• Ya yi fina-finai da yawan gaske
• Ya zama uban daban uwayen daba a fina-finai 😅
• Ya sheka a 2020 sakamakon bugun zuciya
• 'Yan Telugu sun girgiza saboda mutuwarsa

A wane fim ka fi tunawa da shi?
Ni: Kai tsaye Masheki (Faranti Waaaku) 😆

Waye ya tuna da wannan?Jarumi Vikram - karshen jarumai
02/08/2026

Waye ya tuna da wannan?
Jarumi Vikram - karshen jarumai

Address

Abubakar Tafawabalewa University Bauchi
Abuja
740102

Telephone

+2348108254387

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Muryar Al'umma TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Muryar Al'umma TV:

Shortcuts

Share