15/05/2023
**BILAL BN RABAH ONLINE RADIO**
*SHIRIN LABARUN MAKO*
Yau LITININ: 25, ga watan sha'aban,1444h wanda yayi dai dai 15/ mayu/2023m.
* DA FARKO GA MUHIMMAN KANUNSU*
(1) Wani malamin Addinin musulunci a jihar Bauchi, Mai suna ustaz sulaiman zakariyya (Abu bassam) ya shawarci iyayen Mata da suyi amfani da darrussan da s**a koya a lokacin gudanar da Azumin watan Ramadan.
(2) Shashen malamai Mata na makarantar Bilal BN rabah ya samu Karin sabowan Malama.
(3) An gargadi dalibai tare da Jan kunnensu akan yawan fita daga ajujuwansu a lokacin karatu.
(4)An ja hankalin dalibai akan suna kokarin dage ababen zaman karatunsu da kuma kujerun malamansu.
(5) A wani 6angare kuma An tunatar da dalibai akan suna kokarin xuwa makarantar da Kayan karatu dana rubutu.
(6) Hukumar gudanarwan makarantar Bilal BN rabah tayi Kira da Babban murya,akan dalibai su daina tsayuwa akan hanya ko bin hanyar da ba hanyar tapia gida,da zaran an tashi daga makarantar.
**YANZU KAN MAI SAURARO SAI KA GYARA ZAMA DOMIN JIN CIKAKKAN SU WANDA NI SALISU ABUBAKAR DANDIJA ZAN KARANTU***
(1)Wani malamin Addinin musulunci a jihar Bauchi, Mai suna ustaz sulaiman zakariyya (Abu bassam) ya shawarci iyayen Mata da suyi amfani da darrussan da s**a koya a lokacin gudanar da Azumin watan Ramadan da yawuce,malami Mai karantarwan yayi wannan kiranne a lokacin da yake gudanar da wa'azin koron sallah, a babban Masallacin jumu'ar na Bilal bn Rabah dake nassarawa jahun unguwan dim a nan cikin garin Bauchi, a lokacin gudanar da wa'azin koron sallar yasamu halattar kungiyar Mata masu kula da Massalacin da sauran daukacin al'ummah na unguwani,daga karshe sai malamin Addinin sai yayi Addu'ar da fatan Allah yasaka wa kowq da alkhairi, daga bisani sai Kara da cewa zasu cigada gudanar da wa'azin karshen wata kamar yadda yasaba a ko wani karshen wata.
(2) Shashen malamai Mata na makarantar Bilal BN rabah yasamu sabon malama, Shashen malaman dayane daga cikin malamai masu koyarwa a makarantar,Wanda ya juma Yana bada gudumawansa, a 6angaran aikace -aikace na makarantar. (wakilanmu na makarantar Bilal BN rabah salisu Abubakar Yana tape da cigaban reportan)" Shashen malamai na mata dayane daga cikin Shashen da yake ba gudanarwansa a makarantar,a cikin wannan satin da muke cikine dai makarantar ta gabatarwa da sabowan malaman Mai suna " HAJARA ABDULLAHI" wa daliban makarantar na 6angaren islamiyya wanda tunin malaman tafara gudanar dakaratu,a makarantar daga karshe sai malama Hajara tayi fatan alheri wa makarantar Bilal BN rabah.(karshen reportan kinan salisu Abubakar).
* to an gaisheka*
(3)An gargadi dalibai tare da Jan kunnensu akan yawan fitowa daga ajujuwansu a lokacin da ake gudanar da karatu, wannan gargadi ya fitone daga bakin shugaban makarantar Bilal BN rabah, malam Abdurrahman Yusuf Adam, bisani ganin yadda dalibai s**an baro ajujuwansu sannar daga bisani su cigaba da wasa a farfajiyan makarantar,sai ya tunatar da malaman ajujuwa dasu zawo masu saka ido akan dukkan dalibai domin ganin sun zauna a ajinsu,daga karshe shugaban ya jadda daukan mataki akan haka.
** MAI SAURARO KAI DAI KASHA'AFA KANA SAURARON SHIRIN LABARUN MAKO NE DAKE ZUWA MAKA DAGA NAN SHASHIN LABARU DA AL'AMURAN YAU DA KULLUM NA GIDAN RADIO BILAL BN RABAH**
** TO MADALLAH BARKANMU DA DAWOWA*
(4)An ja hankalin dalibai akan suna kokarin dage ababen zaman karatunsu dana malamansu da zaran antashi a makarantar, wannan Kiran yafitone daga Hukumar makarantan Bilal bn Rabah, sunyi wannan kiranne ganin yadda muke tunkaran damina, a lokacin da yake isar da wannan sakon a wajen taron dalibai na makarantar Wanda akeyinsa a ko wani farkon mako wato ( Assembly),malamin sai ya jadda da matakin da makarantar zata dauka akan dukkan ajujuwan da s**a bar Kayan karatu ajin.
(5) A wani 6angarin kuma an tunatar da dalibai akan suna kokarin xuwa makarantar da Kayan karatu dana rubutu, makarantar tayi wannan kiranne ganin yadda taga kaso 75%na dalibai basa xuwa da Kayan karatu a makarantar,a lokacin da shugaban makarantar Bilal BN rabah malam Abdurrahman Yusuf Adam ya ziyarci wasu ajujuwan a makarantar daga cikin ajujuwan da shugaban ya ziyarta sun hada da 6angari rukunin ajujuwan Haddah Dana islamiyya,daga bisani sai shugaban makarantar yanada wani committee Wanda zai na zagayawa domin ganin ko wani dalibi Yana xuwa da Kayan karatu,Jim kadan bayan tabbatar da committee,sai ta fara gudanar da aikinta nan taki,bisa jagorancin malam zayyad Hussain Idris.
ZAYYAD HUSSAIN Idris sai ya sha alwashen hukunta duk wani dalibin dabaya xuwa da cikikkin Kayan karatu.
(6) Hukumar gudanarwan makarantar Bilal BN RABAH tayi Kira da Babban murya, akan dalibai su daina tsayuwa akan hanya ko bin hanyar da ba hanyar tapia gida ba ,da zaran an tashi daga makarantar, Kiran yafitone daga bakin Shugaban makarantar Bilal BN rabah, shugaban yayi la'akari ne ganin yadda daliban s**a mayar dashi al'adah, sai yasha alwashen hukunta duk daliban da aka same su, a tsaye akan hanya bayan an tashi daga makarantar.
** DAMA WANNAN REPORTAN MUKE KAWO KARSHE LABARUN MAKO SAI WANI MAKO IDAN ALLAH YAKAIMU ZAKUJI MU DA WASU LABARUN NA DABAN**
YANZU KAN AMADADIN DAUKACIN GUDANARWAN MAKARANTAR BILAL BN RABAH DA TAKE KAWO MUKU
SAI EDITORMU NA WANNAN MAKON
ZAYYAD HUSSAIN IDRIS
SAI NI DANA SHIRYA KUMA NA GABATAR
SALISU ABUBAKAR DANDIJA NAKE ALLAH YAKAIMU WANI MAKO LAPIA.