29/10/2022
MATA MUTANENMU
Nasir Almustapha Sheshe ya rubuta:
Yau naci karo da abunda yafarantamin rai Allah ya ƙara ma annabi daraja amin 😍😍
Jiya bayan na fita kasuwa sai kawai naga mai ɗakina ta min magana a WhatsApp. Abban Sultan yau kaji da kifi muke buƙata a gidan. Nace toh kuci mana. Sai tace zaka aiko dasu yanzu ko mu saya anan? Nace ku saya anan ɗin. Tace guda nawa kajin Tarwaɗar, kuma kilo nawa? Cikin gatse nace mata kaji 10 tarwada kilo 5
Tace wow ta tura wasu stickers.
Toh ni dai nasan ban ajiye ko sisi a gidan ba iyaka dai in ta saya da kudinta sai ta dora akan bashin da ake kakaba min na babu gaira babu dalili
Kuma nama san ba zata iya sayen adadin da nayi mata gatse ba. Karkari tayi kuru ta sayi kowanne guda dai dai..
Kuma na kudurce a raina in ta saya bazan biya ba.
Kawai na sauka daga WhatsApp na kashe data ma dan kar muyi dogon zance.
Ga mamakina ina dawowa naga an gama gyara komai kamar yanda na ambata an soya na soyawa anyi farfesun wasu wasu anyi miyi saura kuma ansa a FIRIZA
A Raina nace zanci banza kenan Dan wlh ba biya zanyi ba. Na ɗauki wayata na kira abokina nace kar kaci komai fa yau kazo gidana yar Aljanna ta shirya mana liyafa.
Na kalleta cikin murmushin ƙeta nace ina zoɓo. Tace ai aiki ne yayi yawa amma na siyo five alive. Nace wohoho! Allah Ya baki Aljanna, tace Ameen.
Bayan naje sallar Magariba sai nace bari in biya gidan su amaryar can in karɓo kuɗin ankon dana fidda musu. Maƙociyarmu ce bikinta za'ai kuma ni na fidda ankon nata. Akwai kuɗin turmi 10 da zata bani dama.
Ina biyawa nayi sa'a kuwa ta dawo daga rabon goro nace mata amarsu miko inyi gaba. Tace me fa? nace 45k, tace auho! Baka koma gida bane? Nace daga gidan nake, naje sallar Magariba ne sai na biyo tanan. Tace okay ai tun safe na shiga tace yanzun nan ka fita kasuwa, sai na bata kudin.
TUN JIYA BAYAN MAGARIBA NAKE FAMA DA WANI ABU ME KAMAR ZAZZABI.
BAKINA SAI DACI YAKE.