07/12/2025
DA DUMI-DUMI: Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya miƙa lambar yabo ga Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulƙadir Mohammed, a matsayin gwarzon gwamna da ya yi fice wajen ingantaccen shugabanci da bunƙasa birane.
An ba da wannan karramawa ne a wani baje kolin kimanta ayyukan shugabanni da Ma’aikatar Sakataren Gwamnatin Tarayya ta shirya tare da hadin gwiwar cibiyar Best Strategic Media, wacce ta ƙware wajen tantance ayyukan manyan jami’an gwamnati a faɗin ƙasa.
Shugaban ƙasa Tinubu, wanda Sakataren Gwamnatin Tarayya, George Akume, ya wakilta, ya bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed ya cancanci wannan girmamawa sakamakon kyakkyawan tsare-tsaren sa na ci gaban birane, manufofin da s**a haɓaka tattalin arziki da jin daɗin al’umma, da kuma jajircewarsa wajen gudanar da mulki bisa gaskiya da rikon amana.
A yayin bikin miƙa lambar yabo da aka gudanar a babban dakin taro na Fadar Shugaban Ƙasa, Akume ya jaddada cewa gwamnatin tarayya na maraba da irin gudummawar jagoranci mai inganci da gwamnonin da s**a keɓanta suke bayarwa, yana mai cewa irin waɗannan kyaututtuka na ƙarfafa nagarta da gasa mai kyau tsakanin shugabanni.
Gwamna Bala Mohammed ya yi godiya bisa wannan karramawa, yana mai cewa za ta ƙara masa ƙaimi wajen ci gaba da aiwatar da manyan manufofi da tsare-tsare da ke canza fuskokin birane tare da inganta rayuwar al’umma a Bauchi da ma sauran Arewa maso Gabas.