08/10/2023
!...
Matasan Yobe ta kudu (ZONE "B") daga ƙananan Hukumomi Guda Hudu (4) FIKA, FINE POTISKUM da NANGERE.
Matasan sunyi taron Ƙara wa juna sani da neman hadin kan Junanmu su, domin cigaban yankin da Jihar Yobe baki daya.
Daga Karshe Sunyi Allah wadai da siyasar kabilanci da Ɓangaranci yadda Ya Mamaye yankin, Yakawo Rarrabuwar kai a tsakaninsu Al'umma da kawo Cima baya na hana yankin cigaban Yobe ta kudu ZONE B.
Wannan shine irin chigaba da muke son gani a shiyyar mu na Yobe ta kudu wato ZoneB.
Naji dadin yadda naga fuskokin kusan mafi yawan matasa yan’uwa na a wajen taron yau.
Da yan PDP da APC da NNPP da ma wanda ba su da Jam’iyyah duk suna wajen domin tattaunawa akan chigaban mu baki daya.
Mungode Allah da yadda akayi aka gama lafia tare da fatan Allah yasa abun yadaure.
Wanda s**a zo daga wajen Potiskum muna godia da fatan Allah mayar da kowa gida lafia.
Allah qara hada kawunan mu waje guda.
Allah Ubangiji Yabamu Zaman Lafiya, Ƙaunar Junanmu Mai daurewa, Cigaban Yankunanmu da Jihar Yobe Gabakidaya.
Jinjina ga Matasanmu na Zone B.
8th, October, 2023.