24/10/2025
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un!
Yarinya me ciki, da na muku rubutu jiya, Allah Ubangiji ya mata rasuwa.
Kamar yadda na faɗa muku nayi waya da yayar mijin akan akai yarinyar asibiti, tace mun su a gidan su ba akai mutum asibiti, ruwan rubutu ya wadatar.
Abun da ya faru, jiya da daddare bayan na yi posting abinda ke faruwa, sai gidan mijin s**a ƙwace ma yarinyar waya, wanda hakan tasa ajiya da daddare bamu iya samun gidan da yarinyar take ba, amma dai ta tabbatar mun a taraba take, ibbi LGA, ƙofar ajiya.
Bayan sun karɓe mata waya sai ya kasan ce sun kashe wayar, sannan ita ma yayar mijin sai ta kashe wayar ta.
Yanzu da magriba ina kiran wayar yayar mijin sai ta shiga, kuma ta tabbatar mun cewa yarinyar ta rasu amma kuma yayar mijin taƙi yadda taban address ɗan gidan na su.
Idan akwai wanda zai haɗa ni da jami'an tsaro dan akama wannan mutane, Dan Allah ku taimaka mun.
Ajiya yarinyar ce mun take ji take kamar zata mutu, amma ahaka saboda rashin imani s**a ƙi Kaita asibiti.
Ina da lambar wayar yayar mijin, recording na waya ta da ita, sai lambar wayar yarinyar, da kuma address ɗan da yarinyar ta bani jiya, wanda wasu bayin Allah, s**a je amma basu samu gidan ba.
Zan samuku wasu daga cikin chat ɗina da yarinyar kafin rasuwar ta.
Pls amun sharing ko Allah zai saƙon ya kai ga mahukuntan jahar.
Allah Ubangiji ya gafarta mata.
Waɗan nan azzalumai, Allah ya tona musu asiri.
Dr Abdurrahman DambazauLikitan Magani - Pharmacist Alhassan Mai Lafia Fauziyya D. Sulaiman