Jaridar Bakinka al kalinka

  • Home
  • Jaridar Bakinka al kalinka

Jaridar Bakinka al kalinka Peace and unity in Nigeria

09/06/2022

Ya k**ata duk wani masoyin Atiku Abubakar da Bola Ahmad Tinubu ya nutsu ya karanta wannan rubutun da kyau......

Manyan 'yan jaridu masu bincike ne s**a tattaro dukkannin bayanan, dake dauke da darasin siyasa.

Sunyi kokarin tattaro alaka, k**anceceniya da tarayyar da dan takaran APC Bola Tinubu ya yi da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP.

Bayanin nasu ya kasu kashi-kashi har kashi 10.

Ga bayanan k**ar haka;

1. SHEKARU

A shekarar nan Atiku Abubakar zai cika shekara 76 a Duniya domin a haife shi ne a 1946. Shi kuwa Bola Tinubu a bana ya cika shekara 70 da haihuwa.

Kusan dukkaninsu sa’annin juna ne, tazarar shekara biyar ne tsakanin ‘yan takaran.

2. DUKIYA

Dukkanin ‘yan siyasan biyu su na da arziki, attajirai ne na buga misali, sai dai Bola Tinubu ya yiwa Atiku fintinkau a wurin tara arziki.

Tun kafin shigarsa siyasa, Atiku Abubakar ya kai babban matsayi a aikin kwastam, anyi kiyasin yanzu haka ya mallaki kadara ta kusan Tirilan guda.

Shi ma Bola Tinubu dan kasuwa ne ko kafin ya zama gwamnan Legas, a yanzu haka anyi kisan ya mallaki kadara ta kusan tiriliyan 4.

Tinubu shine dan siyasar da yafi kowane dan siyasa tarin arziki a Najeriya.

3. FARA SIYASA

Inda wadannan mutane s**a kara yin tarayya shi ne sun shiga siyasa ne kusan a lokaci daya.

A 1992 aka fara jin sunan Atiku da Tinubu da kyau a Najeriya.

Bola Tinubu ya zama Sanata a lokacin, shi kuwa Atiku ya yi takarar shugaban kasa. Tinubu yana tare da su MKO Abiola, Atiku yaronsu Shehu Yar'adu'a ne.

4. SAMUN KUJERAR GWAMNATI

Bayan an dawo farar hula a 1999, Wazirin Adamawa da Jagaban s**a lashe zaben gwamna a jihohinsu na Adamawa da Legas a karkashin AD da PDP.

Bola Tinubu ya yi shekaru takwas yana gwamna, shi kuwa Atiku ya samu damar tafiya A*o Villa.

5. RASA MADAFAN IKO

Daga watan Mayun 2007 zuwa yanzu, mutanen nan biyu ba su rike wani mukami a gwamnati ba.

Shekaru 15 kenan da Atiku Abubakar ya fita daga A*o Villa.

Shi ma Bola Tinubu ya bar kujerar gwamnan Legas a 2007, rana daya da abokin takaransa na yanzu.

6. CIN BURIN MULKI

Inda wadannan ‘yan takara s**a sake yin k**a da juna a siyasa shi ne dukkaninsu sun dade su na neman yadda za su samu damar shugabantar Najeriya.

Atiku ya yi takara a 1992, 2007, 2011, 2015, da 2019, yayin da shi kuma Tinubu yake ta jiran 2023.

7. ZARGIN RASHIN GASKIYA

Ana yi wa ‘yan siyasan biyu kallon marasa gaskiya wadanda s**a amfana da baitul mali ko su na kan yi a dalilin kusancin da s**a samu da kujerun gwamnati.

8. AKIDAR SIYASA

Masu nazarin siyasa a Najeriya su na cewa jirgi daya ya dauko ‘dan takaran na jam’iyyar PDP da abokinsa na APC domin duk sun yi imani da tsarin jari hujja.

9. RASHIN KAUSHI DA RA’AYIN RIKAU KO ADDINI

An tabbatar da Atiku da Tinubu a matsayin wadanda ba su da ra’ayin rikau a kan abin da ya shafi lamarin addini da kabilanci ko yanki.

Bola Tinubu ya na auren Kirista, Atiku kuwa ya auri Bayarabiya da Inyamura a cikin matansa.

10. TARAYYA A JAM’IYYA

Kafin su raba jiha a siyasa, Wazirin Adamawa da Asiwaju Tinubu sun zauna tare a karkashin jam’iyyun SDP a 1992, ACN a 2007 da jam'iyyar APC a 2015.

Bayan Atiku ya yi takara ne ya bar ACN a 2007, sannan ya sauya-sheka daga APC a 2018.

Gareku masoyan kowane bangare, ya rage naka kasan irin siyasar da zaka yi, domin dukkansu kusan halin su daya ne, ba suda wani bambanci a tsakanin su.

Kada ka bari siyasar 2023 ta rufe maka ido, ka yita fada da 'yan uwanka ko abokanan ka, akan 'yan siyasar.

Kada ka bari a chusa maka kabilanci, ko wani abu na daban da zai sa kaji haushin dan uwanka akan su.

Kowa yabi ra'ayin shi na siyasa, domin ba don lada ake siyasa ba.

Babban fatanmu, Allah ya zama mana mafi Alkhairi a garemu, mun barwa Ubangiji zabi shi yafi mu sanin mafi Alkhairi a garemu.

~ Comr Abba Sani Pantami

A yau Ne muka samu tattaunawa da shahararriyar matashiyar Nan wacce kukafi sani da Khadeeja babangida sulaiman, Mun tatt...
17/05/2022

A yau Ne muka samu tattaunawa da shahararriyar matashiyar Nan wacce kukafi sani da Khadeeja babangida sulaiman, Mun tattaunane da ita dangane da Abun da yake damun Yan mata A wannan zamani, Kamar yadda matashiyar tayi mana bayani cewan Babu Abun da Ake taka rawar gani Dan gane da lalacewan Yara mata irin Rashin Sana'aryi, duk da matashiyar tayi mana bayani cewan wasu matan kawai kwadayin Abun duniya ne yake jawo Hakan, wasu Kuma tabbas suna cikin tsanani ne, matashiyar tana kiraga Yan mata Yan uwanta da su tashi sunemi nakansu s**ama sana'a domin gujewa ga fadawa Halaka. Inafatan sauran Yan mata zasuji su gyara.

13/05/2022
(Bakinka al kalinka)    Kowani Dan siyasa a Nigeria akullum in yafito takara ba abun da ake fara gaya wa talakawa shine ...
25/04/2022

(Bakinka al kalinka)
Kowani Dan siyasa a Nigeria akullum in yafito takara ba abun da ake fara gaya wa talakawa shine insha Allah in munci damu kawo cigaba a fanin ilimi damu mai da karatun talaka yazamo

kyauta toh ya kuke ganin fannin ilimi a Nigeria a yanzu cigaba ake samu ko cibaya

BAKINKA AL KALINKA✍️

(Bakinka al kalinka)Sau da yawa a Nigeria  yawan cin yansiyasa s**an fito a lokacin takarar zabe suyi al kawari wa talak...
20/04/2022

(Bakinka al kalinka)Sau da yawa a Nigeria yawan cin yansiyasa s**an fito a lokacin takarar zabe suyi al kawari wa talakawa bayan sunci kuma su juya baya kuma su gagara cika wannan al kawarin da s**a dauka toh miye ra a yinku a zaben bana, ko kunaga akwai wani Dan siyasan dazai fito yamuku dadin baki ko aa
Bakinka al kalinka✍️

19/04/2022

Yi hankali da bakinka domin yakan jawo adaure dukkan jikinka ma ana bakinka al kalinka👂

19/04/2022

DUNIYA MAKARANTA

Address


Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Jaridar Bakinka al kalinka posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Jaridar Bakinka al kalinka:

Shortcuts

  • Address
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share