19/09/2026
TUNA BAYA: FURUCIN MARIGAYI SARKIN KANO ADO BAYERO KAN GINA COCI A BUK.
“Ko Jonathan bai isa ya gina Coci a BUK ba”
Zaman Babbar Kotun Shari’a (Federal High Court) da ke babban birnin tarayya Abuja, a kan ƙarar da Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa (CAN) ta kai Masarautar Kano, saboda Mai Martaba Sarkin Kano, Alh. Dr. Ado Bayero, ya sa an rushe wata Coci da ake ginawa a cikin tsohuwar Jami’ar Bayero Kano (BUK).
A zaman kotun da aka yi a ranar Litinin, 3 February 2014, kwanaki 123 kafin rasuwarsa (Ado Bayero 06 June 2014), kotu ta nemi Mataimakin Shugaban Jami’ar Bayero, Prof. Rasheed, da wakilin Ƙungiyar Kiristoci ta Ƙasa, da kuma Mai Martaba Sarkin Kano, da su bayyana a gabanta, a zaman kotun. An ga Prof. Rasheed da Mataimakin Shugaban CAN sun mike tare da Lauyoyinsu, amma ba a ga Mai Martaba Sarki ba.
Daga nan sai jagoran Alkalan kotun, Justice Alakola Nweri, ya ce, da yake muna da sauran mintuna 10 kafin fara shari’ar, za mu jira zuwan Mai Martaba Sarkin kafin waɗannan mintocin.
Daga nan sai Justice ya dubi Prof. Rasheed ya ce, a baya Kotu ta ba ku umarnin Gina Coci a Jami’ar Bayero, ko kun bi umarnin kotu?
Prof. Rasheed ya ce, ƙwarai kuwa mun bi umarnin Kotu, don sai da ginin Cocin ya kai linta, sannan Mai Martaba Sarkin Kano ya ba mu umarnin tsayar da aikin, daga baya kuma sai ga Mai Girma Galadiman Kano, Alh. Tijjani Hashim, ya jagoranci Rushe ginin gaba ɗaya. Justice ya ce, kuna nufin kenan kun yi watsi da umarnin kotu kun bi na Sarki?
Prof. Rasheed ya ce, ƙwarai kuwa, saboda Sarki Ubanmu ne, kuma shi ne Sarki mai daraja ta ɗaya a ƙasar nan bayan Sarkin Musulmi, saboda haka, ba za mu iya ƙin yi masa biyayya ba.
Daga nan sai Justice ya umarci Prof. Rasheed da ya zauna. Justice ya ce da wakilin CAN, ka ji abin da ya faɗa, kana da abin cewa?
Sai ya ce, Eh, wakilin CAN ya ce, gaskiya ne hukumar Makarantar Jami’ar Bayero ta fara gina Cocin, aka hana su, saboda haka muke roƙon wannan kotu da ta hukunta Sarkin Kano bisa shiga hurumin da ba nasa ba. Daga nan shi ma