18/08/2026
Rundunar 'Yan Sanda Ta Kwato Kayan Jirgin Kasa Da Aka Sace A Bauchi, Ta K**a Mutum Daya
Rundunar 'Yan Sandan Jihar Bauchi ta samu nasarar kwato saitin karfen dogon jirgin kasa (railway sleepers) da aka sace, sannan ta k**a wani mutum daya mai suna Abubakar Sanusi da ake zargi da hannu a lamarin.
Rundunar ta samu rahoton sirri kan satar da lalata kayan jirgin kasa a cikin birnin Bauchi.
Jami'an 'yan sanda na Sashen 'A' (A Division Township) sun gudanar da samame a wani gida na kashin kansa da ke Doya Quarters, inda s**a samu nasarar kwato kayayyakin da aka boye tare da k**a wanda ake zargin.
A yanzu haka ana ci gaba da bincike mai zurfi domin gano sauran mambobin kungiyar da s**a tsallake rijiya da baya.
Rundunar ba za ta saurarawa kowa ba wajen kare dukiyar gwamnati, kuma duk wanda aka samu da hannu a lalata ko satar kayan jama'a zai fuskanci fushin doka.
Rundunar ta kuma bukaci al'umma da su ci gaba da ba hukumomi hadin kai ta hanyar kai rahoton duk wani abun zargi.
A s duguri media tv
18-8-2026