15/05/2023
KOTU TA TURA SHEKH IDRIS ABDULAZIZ GIDAN YARI A JIHAR BAUCHI.
_____________
Kotu ta tura malam Dr. Idris Abdul’aziz Dutsen Tanshi gidan yari bisa zargin furta kalaman ta da zaune tsaye.
Malamin wanda ya amsa gayyatar ‘yansanda a yau Litinin, daga bisani sun gurfanar da shi a gaban kotu bisa zargin kalaman rashin da’a da ka iya barazana ga zaman lafiya.
yansandan sun gurfanar da shi ne a gaban kotun Majistire ta 1 kamar yadda leadership ta tabbatar.
Hukumar Shari'a ta jihar Bauchi ce ta fara tuhumar sa kan wani furucin sa da ya tayar da ƙura sosai ba ma a Jihar Bauchi ba a duk faɗin Nijeriya saboda abin da ya hukumar tace ya fadi ce'wa' Ko Manzon Allah ma ba su bukatar taimakonsa.” wanda aka nemi ya janye
Kotun ta tura shi zuwa gidan yarin ne kafin daga bisani a ci gaba da sauraron karar da ‘yansanda s**a shigar a gobe Talata.
Da yake tabbatar da kamun da aka yi wa malamin, Shugaban kungiyar Matasa Masu Neman Hadin Kan Malamai Da Cigaban Al’ummar Jihar Bauchi, Yusuf A. Jibrin, ya bayyana cewar malamin ya je wajen ‘yansanda domin amsa gayyatar da s**a yi masa ne amma daga bisani s**a gurfanar da shi a gaban kotu.
“Na san da gayyatar da aka yi wa Malam daga hukumar ‘yansanda wanda a yau da safe (Litinin) aka tabbatar mana da cewa Malam ya amsa wannan gayyatar. A da kam ma mun shirya har da ni muka ce za mu je mu yi masa rakiya. Amma da muka yi waya da Allaramma sai ya ce mana a’a malam ya ce bai bukatar kowa ya je. Zai je shi kadai da direba da Malam Ya’u.
“Dazu kuma sai shi Allaramma ya kira ni yake ce min an kai Malam gidan Yari. Yake ce min har an kaishi kotu, kotu kuma ta turashi gidan yari.”
Yusuf ya ce, dukkanin abun da ake cajin malamin nasu a kai abu ne da ya shafi akidarsu, “Wannan maganar da malam ya yi akidarmu ne a kai kuma muke fatan Allah ya karbi rayukanmu, kuma manufarmu daya kuma a kanta muke.”
A cewarsa, malaminsu ya koyar da su zaman lafiya da kwanciyar hankali, don haka za su bi dukkanin matakan da s**a dace a doron shari’a wajen nema wa malaminsu hakkinsa.
Shugaban, ya bayyana cewar su na ta kokarin kwantar wa almajiran malamin da hankali yayin da ake ci gaba da bin matakan da s**a dace wajen ganin malamin ya samu ‘yanci.
“Muna kira ga mutanenmu da su kasance cikin zaman lafiya kuma za mu bi lamarin a bisa tsarin doka domin mu tabbatar mun bi kadin abun da aka mana,” Yusuf A. Jibrin ya shaida.
Bayan kalaman malamin ne, hukumar shari’a ta jihar Bauchi ta aike da wasikar gayyata ga Malam Idris domin ya bayyana a gaban malamai domin wanke kansa ko kare kansa sai dai bayan ca! da malaman da ke goyan bayansa s**a yi hakan ya gagara ba tare da an samu yin mukabalar ba.
Ledership Hausa.