Duniya Voice TV

Duniya Voice TV Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Duniya Voice TV, Media/News Company, Bauchi.

LABARIN GAGGAWA: Kotu Ta Hana INEC Amincewa da Kongres na Rikon Kwarya na ADCWata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, kark...
29/04/2026

LABARIN GAGGAWA: Kotu Ta Hana INEC Amincewa da Kongres na Rikon Kwarya na ADC
Wata Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, karkashin jagorancin Mai shari’a Joyce Abdulmalik, ta haramtawa Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (Independent National Electoral Commission – INEC) amincewa ko shiga cikin duk wani kongres na jihohi da shugabancin rikon kwarya na jam’iyyar ADC ke shiryawa.

A cikin hukuncin da ta yanke, kotun ta kuma hana tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata David Mark, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar, tsoma baki cikin ayyuka da wa’adin halascin shugabannin jam’iyyar na jihohi da aka zaba.

Umarnin ya biyo bayan karar da Norman Obinna da wasu mutum shida s**a shigar, suna wakiltar shugabannin jam’iyyar ADC na jihohi da kwamitocinsu na gudanarwa.

Masu karar sun kalubalanci sahihancin shugabancin rikon kwarya na kasa, suna masu cewa wannan tsari ba shi da hurumin kundin tsarin mulkin jam’iyyar na shirya kongres na jihohi ko nada kwamitoci domin hakan.

Sun bukaci kotu ta tabbatar da halascin shugabannin jihohi da aka zaba da kuma wa’adinsu, tare da dakatar da duk wani tsari na daban da zai iya tauye su.

Wannan hukuncin na wucin gadi na da nufin tabbatar da matsayin da ake ciki (status quo) domin kauce wa duk wani mataki da zai iya shafar shari’ar kafin a yanke hukunci na karshe.

Mai shari’a Abdulmalik ta bayyana cewa ta ga karar na da inganci, tana mai cewa muhimmin batu shi ne ko wadanda ake kara daga na biyu zuwa na shida, ciki har da Sanata Mark, suna da hurumin kundin tsarin mulki ko na doka na karbar ikon da ya dace da zababbun shugabannin jihohin ADC.

Ta ce sashe na 223 na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanadi cewa dole ne jam’iyyun siyasa su rika gudanar da zabuka lokaci-lokaci bisa tsarin dimokuradiyya, yayin da sashe na 23 na kundin tsarin mulkin jam’iyyar ya kayyade cewa jami’an kasa da na jihohi za su rike mukami na wa’adi biyu kacal, wato shekaru takwas.

Dangane da hujjar cewa batun ya shafi harkokin cikin gida na jam’iyya, kotun ta ce duk da cewa a ka’ida kotu ba ta tsoma baki, amma idan an samu zargin karya dokar kundin tsarin mulki ko wata doka, to wajibi ne kotu ta shiga tsakani.

Kotun ta jaddada cewa dole ne jam’iyyun siyasa su bi kundin tsarin mulkinsu yadda ya kamata, kuma kotu na da ikon shiga idan an karya wannan tanadi.

Ta kuma gano cewa tsarin da wadanda ake kara s**a bi, ciki har da nada “kwamitin kongres”, ba shi da tushe a kundin tsarin mulkin jam’iyyar.

Saboda haka, kotun ta tabbatar da cewa wa’adin shugabannin jihohi na jam’iyyar na nan daram, kuma dole ne a bar su su kammala wa’adinsu. Ta kuma ce su kadai ne ke da ikon shirya kongres na jihohi.

Kotun ta soke nadin kwamitin tare da hana INEC amincewa da duk wani kongres da aka shirya ta hannunsa.

Haka kuma, kotun ta hana Sanata Mark da sauran wadanda ake kara shirya duk wani kongres ko babban taro da ya saba wa kundin tsarin mulkin jam’iyyar, tare da hana su daukar duk wani mataki da zai iya tauye ikon shugabannin jihohi.

Wadanda aka shigar da kara sun hada da jam’iyyar ADC, Sanata David Mark, Patricia Akwashiki, Malam Bolaji Abdullahi, Ogbeni Rauf Aregbesola, Oserheimen Osunbor, da kuma INEC.

Masu karar sun dage cewa, bisa kundin tsarin mulkin jam’iyyar da na kasa, wa’adin shugabannin jihohi yana nan har sai an gudanar da sahihin kongres, kuma duk wani yunkuri na kauce musu na tauye dimokuradiyyar cikin gida.

Sai dai wadanda ake kara sun bukaci kotu ta yi watsi da karar, suna masu cewa batun na cikin harkokin cikin gida na jam’iyya ne, ba ya cikin hurumin kotu, sannan masu karar ba su da hurumin shigar da kara.

Kan batun hurumin kotu, Mai shari’a Abdulmalik ta ce shari’ar ta shafi harkokin INEC, don haka tana karkashin ikon Babbar Kotun Tarayya bisa sashe na 251 na kundin tsarin mulki.

Game da batun cewa ba a bi hanyoyin sasanta rikici na cikin jam’iyya ba, kotun ta ce yanke hukunci a kai a wannan mataki zai zama yanke hukunci kan muhimman batutuwa kafin lokaci.

Kan batun hurumin masu karar, kotun ta ce huruminsu ya samo asali ne daga zargin take hakkin da s**a gabatar, kuma kasancewar suna da matsala iri daya ya sa karar wakilci ta dace.

Wani Lebura Ne Yayi Aure Shi Ne Akayi Bulon Tuwan Masara 😂😂😂.Idan Kaine a sana'arka tuwon me za'ayi ?.
28/04/2026

Wani Lebura Ne Yayi Aure Shi Ne Akayi Bulon Tuwan Masara 😂😂😂.

Idan Kaine a sana'arka tuwon me za'ayi ?.

28/04/2026

SIYASA: An Ƙara Ƙarfafa Takarar Gwamnan Shehu Buba Yayin da Abokai da Abokan Hulɗa S**a Tara Naira Miliyan 50 Don Saya Masa Fom ɗin Takara A Bauchi

DA DUMI DUMI: Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Umarci Masu Rike da Mukaman Siyasa da ke Sha’awar Tsayawa Takarar Zabe Su Ajiye ...
22/04/2026

DA DUMI DUMI: Gwamnatin Jihar Bauchi Ta Umarci Masu Rike da Mukaman Siyasa da ke Sha’awar Tsayawa Takarar Zabe Su Ajiye Mukamansu Kafin 24 ga Afrilu, 2026

Gwamnatin Jihar Bauchi ta umarci dukkan masu rike da mukaman siyasa da ke da niyyar tsayawa takara a zabukan fidda gwani masu zuwa da su ajiye mukamansu kafin ko a ranar 24 ga watan Afrilu, 2026.

Umarnin na kunshe ne cikin wani bayani da gwamnatin ta fitar, inda ta jaddada cewa matakin ya dace da tanade-tanaden dokar zabe, tare da nufin tabbatar da gaskiya da adalci a tsarin zaben.

The Islamic movement in Nigeria, popularly known as Shi’ites, has called on Muslims and Christians across the world to u...
20/04/2026

The Islamic movement in Nigeria, popularly known as Shi’ites, has called on Muslims and Christians across the world to unite and consistently stand against oppression in order to promote justice and improve living conditions globally.

    BY KHALID IDRIS DOYA, Bauchi   The Islamic movement in Nigeria, popularly known as Shi’ites, has called on Muslims and Christians across the world to unite and consistently stand against oppression in order to promote justice and improve living conditions globally.   The wife of the leader...

17/04/2026

Sakon Sheikh A A Imam Zuwa Ga Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed

14/04/2026
14/04/2026

DA DUMI-DUMI: Babbar Kotun Tarayya ta bayar da Belin El-Rufai
...Ayau News

DA ƊUMI-ƊUMI: Tasirin Dakatar da Harkokin Kasuwancin Dabbobi a BauchiBayan umurnin dakatar da saye da sayar da dabbobi a...
12/04/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: Tasirin Dakatar da Harkokin Kasuwancin Dabbobi a Bauchi

Bayan umurnin dakatar da saye da sayar da dabbobi a wasu kasuwanni a Jihar Bauchi na wani lokaci, sakamakon matsalolin tsaro da ake fuskanta, wanda gwamnatin jihar ta sanar a makon da ya gabata, al’amura sun fara sauyawa a wasu kasuwanni.

Rahotanni sun nuna cewa, ɓangaren dabbobi (tike) na kasuwar Alkaleri ya kasance babu cunkoso da zirga-zirga kamar yadda aka saba, lamarin da ke nuna tasirin wannan mataki da aka ɗauka.

Matakin na zuwa ne a wani yunƙuri na inganta tsaro da dakile ayyukan da ka iya janyo barazana a yankunan da abin ya shafa.

Al’umma na ci gaba da fatan Allah Ya kawo ƙarshen wannan fitina tare da dawo da zaman lafiya a jihar.

DA ƊUMI-ƊUMI: APC a Bauchi ta shirya karɓar Gwamna Bala Mohammed idan ya sauya sheƙaJam’iyyar All Progressives Congress ...
10/04/2026

DA ƊUMI-ƊUMI: APC a Bauchi ta shirya karɓar Gwamna Bala Mohammed idan ya sauya sheƙa

Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) reshen Jihar Bauchi ta bayyana shirinta na karɓar Gwamnan jihar, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, idan har ya yanke shawarar sauya sheƙa daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) zuwa APC.

APC ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa, inda ta ce ƙofarta a buɗe take ga duk masu sha’awar shiga jam’iyyar, ciki har da gwamnan jihar.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa Gwamna Bala Mohammed na shirin ficewa daga PDP zuwa wata jam’iyya.

Sai dai har zuwa yanzu, babu wata sanarwa a hukumance daga gwamnan da ke tabbatar da wannan zargi.

HOTUNA: Gwamna Bala Mohammed tare da tsohon ministan ilimi Malam Adamu Adamu yayin ziyarar girmamawa da gwamnan ya kai m...
09/04/2026

HOTUNA: Gwamna Bala Mohammed tare da tsohon ministan ilimi Malam Adamu Adamu yayin ziyarar girmamawa da gwamnan ya kai masa a gidansa da ke Abuja, inda s**a tattauna kan muhimman batutuwan ci gaban kasa da siyasa.

09/04/2026

Wasu Matasan jam’iyyar APC sun bayyana kansu a matsayin cikakkun ‘yan jam’iyyar, tare da maraba da kiran Gwamna Bala Mohammed da ya koma jam’iyyar.

Address

Bauchi

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Duniya Voice TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Duniya Voice TV:

Share