Giade Daily Post

Giade Daily Post Contact information, map and directions, contact form, opening hours, services, ratings, photos, videos and announcements from Giade Daily Post, Media/News Company, Giade Local Government, Bauchi.

Dubban jama’a sun halarci jana’izar gawar Ali Reza Tangsiri, kwamandan rundunar sojojin ruwa ta IRGC, tare da wasu da ak...
01/04/2026

Dubban jama’a sun halarci jana’izar gawar Ali Reza Tangsiri, kwamandan rundunar sojojin ruwa ta IRGC, tare da wasu da aka kashe a hare-haren haɗin gwiwar Amurka da Isra’ila.

📸 TLN Hausa

Yau tun safe mu ke jin cewar sojojin Chechnya sun shirya shigarwa Iran in har Amurka ta je da sojoji yakar Iran. Muslmi ...
01/04/2026

Yau tun safe mu ke jin cewar sojojin Chechnya sun shirya shigarwa Iran in har Amurka ta je da sojoji yakar Iran.

Muslmi ne su Ahlusunnah daga yankin Russia, kuma sun ce wannan yaki na Addini ne, sam ba za su bari ba.

Wadannan mayaka sun gwabza da Russia ma, sannan su ka sasanta finally a 2009. Yan bala'i mai kyau ne!

Allahu Akbar!

A cikin ƴan sa'o'in da s**a wuce, an kai manyan hare-hare da dama inda Iran ta harba makamai masu linzami sau 5 zuwa 6, ...
01/04/2026

A cikin ƴan sa'o'in da s**a wuce, an kai manyan hare-hare da dama inda Iran ta harba makamai masu linzami sau 5 zuwa 6, sannan HZL ma ta ƙara da manyan hare-haren rokoki guda biyu. Wadannan hare-hare sun afkawa wurare da dama a lokaci guda kan muhimman wurare a Muzra’ila.

An ji fashe-fashe har a Kuwait, yayin da ƙararrawar gaggawa ke ta tashi a yankunan arewacin Falasdinu da Muzra’ila ta mamaye ta zuba mutanen ta a wurin, ciki har da Tel Aviv da sauran manyan birane.

Haka kuma, an kai hari a Kuwait, Erbil, da Bahrain, inda aka samu fashe-fashe da dama. Wasu sansanonin Amurk@ a Dubai ma sun fuskanci hari, wanda hakan ya kawo cikas ga ayyukansu.

A kudancin Lebanon, mayaƙan HZL na ci gaba da ƙoƙarin kare yankinsu duk da hare-haren da ake kai musu. Sun kai farmaki kan sojojin Muzra’ila, har ma s**a harbo wani jirgin sama mai saukar ungulu a sararin Yaroun.

Hare-haren rokoki sun lalata gine-gine da dama a arewacin yankin, musamman a Kiryat Shmona da kewaye, yayin da fashe-fashe ke ci gaba a wasu wuraren na Muzra’ila.

A tsakiyar yankin, hare-haren Iran sun kawo cikas ga rayuwar fararen hular Muzra’ila. An harba makamai masu ƙarfi zuwa Tel Aviv da kewaye, wanda ya haddasa rushewar gine-gine da lalacewar ababen more rayuwa.

Ana ci gaba da jin ƙararrawa a wurare da dama, kuma an umarci mutane da su ci gaba da zama a ramuka saboda hatsarin da ke akwai. Wannan na daga cikin manyan hare-haren da aka taɓa gani tun bayan fara wannan yaƙi.

A yanzu haka, ana ci gaba da wani sabon hari (na bakwai), inda ake sake harba makamai zuwa wurare daban-daban na Sojin Amurk@ da muhimmanci wuraren Muzra’ila.

Hoton dake ƙasa wata ma'aikatar tsaron sojan Muzra’ila ne ke ci da Wuta sakamakon hare-haren Iran.

DA DUMI-DUMI: INEC ta cire shugabannin ADC karkashin David Mark daga shafinta na yanar gizo Hukumar zaɓe mai zaman kanta...
01/04/2026

DA DUMI-DUMI: INEC ta cire shugabannin ADC karkashin David Mark daga shafinta na yanar gizo

Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) ta sanar da cewa ta daina amincewa da kowanne daga cikin bangarorin jam’iyyar ADC biyu, wanda David Mark ke jagoranta da kuma na Rafiu Bala, bayan nazarin hukuncin kotun ɗaukaka kara da aka yanke a ranar 12 ga Maris, 2026.

A cikin wata sanarwa da Shugaban sashen yaɗa labarai da wayar da kai na INEC, Mohammed Kudu, ya sanya wa hannu, hukumar ta ce daga yanzu ba za ta ƙara karɓar kowanne irin wasiƙa daga kowanne bangare ba.

Haka kuma, INEC ta bayyana cewa ba za ta yi hulɗa da kowanne bangare ba, kuma ba za ta sa ido kan taruka, zaɓukan cikin gida (congresses), ko manyan tarukan jam’iyyar (conventions) na bangarorin biyu ba, har sai kotu ta yanke hukunci kan rikicin.

Bugu da ƙari, hukumar ta sanar da cewa za ta cire sunan David Mark daga kundin bayananta na yanar gizo.

Rahotanni sun nuna cewa rikicin ya samo asali ne bayan Rafiu Bala, wanda a baya ya kasance mataimakin shugaban jam’iyyar ADC kafin kwamitin riko karkashin jagorancin David Mark ya karɓi ragamar jam’iyyar, ya garzaya kotu domin ƙalubalantar sahihancin shugabancin sabon kwamitin.

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dage ziyararsa zuwa Ogun, zai tafi Jos domin jajanta wa waɗanda hare-hare s**a shafa....
01/04/2026

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dage ziyararsa zuwa Ogun, zai tafi Jos domin jajanta wa waɗanda hare-hare s**a shafa.

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa Tinubu zai fara ziyarar jihohi huɗu ne daga Plateau, inda zai kai ziyara a Jos domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar kan hare-haren da s**a yi sanadin asarar rayuka.

Daga nan, shugaban zai wuce Lagos domin gudanar da bukukuwan Good Friday, kafin ya tafi Ogun a ranar 4 ga Afrilu domin kaddamar da filin jirgin sama na kaya da wasu ayyukan ci gaba.

Haka kuma zai kaddamar da wasu muhimman ayyukan more rayuwa a Lagos, ciki har da gadar Ojota/Opebi da wasu gine-gine na gwamnati.

Kafin ya koma Abuja, shugaban zai kai ziyara Bayelsa a ranar 10 ga Afrilu domin kaddamar da ayyukan da gwamnatin jihar ta kammala.

SPONSORED ‎CI GABA A FANNIN YADA LABARAI A JIHAR BAUCHI ƘARƘASHIN JAGORANCIN HON. USMAN SHEHU USMAN‎Mai girma Kwamishina...
01/04/2026

SPONSORED

‎CI GABA A FANNIN YADA LABARAI A JIHAR BAUCHI ƘARƘASHIN JAGORANCIN HON. USMAN SHEHU USMAN

‎Mai girma Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na Jihar Bauchi, Hon. Usman Shehu Usman (Wamban Giade), tun bayan hawansa kujerar wannan ma’aikata, an samu gagarumin ci gaba da nasarori a fannin yada labarai da sadarwa a jihar Bauchi.

‎Wasu daga cikin muhimman abubuwan da s**a tabbatar da wannan ci gaba sun haɗa da:

‎Inganta Harkokin Sadarwa na Gwamnati:
‎Kwamishinan ya tabbatar da ingantacciyar sadarwa tsakanin gwamnatin jiha da al’ummar Jihar Bauchi, ta hanyar amfani da sabbin dabarun yada bayanai na zamani.

‎Karfafa Gidajen Rediyo da Talabijin:
‎Gwamnatin jihar ta ƙara zuba jari a kafafen watsa labarai na gwamnati kamar Bauchi Radio Corporation (BRC) da Bauchi Television Authority (BATV) domin inganta shirye-shirye masu amfani da kuma fadakar da al’umma.

‎Shigar da Fasahar Zamani:
‎An fara amfani da dandamali na intanet da kafafen sada zumunta wajen isar da saƙonnin gwamnati cikin sauƙi, lamarin da ya ƙara kusantar gwamnati da jama’a, musamman matasa.

‎Haɗin Gwiwa da Kafafen Yada Labarai Masu Zaman Kansu:
‎Hon. Usman Shehu Usman (Uban Doman Giade) ya samar da kyakkyawar alaƙa da ‘yan jaridu da kafafen yada labarai masu zaman kansu domin tabbatar da watsa sahihan bayanai.

‎Shirye-shiryen Fadakarwa da Ilmantarwa:
‎Ya jagoranci shirye-shiryen wayar da kan jama’a game da ayyukan gwamnatin Sanata Bala Abdulkadir Mohammed (Kauran Bauchi), musamman a bangaren raya karkara da ci gaban matasa.

‎Karin sabbin gidajen Rediyo a jihar Bauchi: Bugu da ƙari, zuwan Hon. Usman Shehu Usman (Wamban Giade) kan wannan kujera yasa za'ayi ƙarin sabbin gidajen rediyo a wasu ƙananan hukumomin dake Jihar Bauchi, ciki har da Ƙaramar Hukumar Giade.

‎Daga ƙarshe, muna yi masa addu’a da fatan alheri, Allah Maɗaukakin Sarki ya saka masa da alkhairi, Ya biya masa dukkanin buƙatunsa na alheri a duniya da lahira, albarkacin Annabi Muhammad (S.A.W)

‎Daga: Habu Ibrahim Giade

Isra’ila: Netanyahu ya ce manufar yaƙin ita ce ɗaga Isra’ila zuwa ƙasar mai ƙarfin tasiri a duniyaFirayim Minista Benjam...
01/04/2026

Isra’ila: Netanyahu ya ce manufar yaƙin ita ce ɗaga Isra’ila zuwa ƙasar mai ƙarfin tasiri a duniya

Firayim Minista Benjamin Netanyahu ya bayyana cewa rikicin da ake yi da Iran wani ɓangare ne na ƙoƙarin faɗaɗa ƙarfin Isra’ila domin ta zama ƙasa mai tasiri a yankin da ma duniya baki ɗaya.

Ya jaddada cewa ayyukan da ake ci gaba da yi suna daidaita da wata doguwar manufa ta ƙarfafa matsayin Isra’ila a idon duniya.

Ana sa ran wannan furuci zai ƙara tayar da muhawara kan ainihin manufofin yaƙin da kuma yiwuwar sakamakonsa na dogon lokaci.

Gwamna Bala Mohammed Yana Da Zabi Biyu Na Jam'iyyu APC Ko ADC Wacce Kuke Fatan Ya Shiga?
01/04/2026

Gwamna Bala Mohammed Yana Da Zabi Biyu Na Jam'iyyu APC Ko ADC Wacce Kuke Fatan Ya Shiga?

Shugaban APC tare da Gwamna Abba Kabir Yusf Sun Gana da Gwamna Bala Mohammed a yauShugaban jam’iyyar All Progressives Co...
01/04/2026

Shugaban APC tare da Gwamna Abba Kabir Yusf Sun Gana da Gwamna Bala Mohammed a yau

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na kasa, Nentawe Yilwatda, tare da gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, sun kai ziyara ga gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, a fadar gwamnati da ke Bauchi.

Rahotanni sun bayyana cewa an dauki ziyarar a matsayin ta kashin kai, domin ba a fitar da wata sanarwa ga manema labarai ba, haka kuma ba a yi wata hira da manema labarai ba bayan kammala ganawar.

Kotu ta tsare direban matar Sarki Muhammadu Sanusi II bisa zargin sataWata kotun majistare da ke Nomansland a karamar hu...
01/04/2026

Kotu ta tsare direban matar Sarki Muhammadu Sanusi II bisa zargin sata

Wata kotun majistare da ke Nomansland a karamar hukumar Fagge, jihar Kano, ta bayar da umarnin tsare direban matar Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, tare da wasu mutum biyu bisa zargin satar wayar matar sarkin, da kudade da wasu kayayyaki.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito wadanda ake tuhuma sun hada da Sulaiman Yakubu Kulkude, Idris Musa da Abdullahi Usaini, inda aka gurfanar da su kan tuhume-tuhume uku da s**a hada da hadin baki, sata da karbar kayan sata.

Alkalin kotun, Mai shari’a Halilu Abdurahman, ya amince da bayar da beli ga wadanda ake tuhuma tare kuma da dage shari’ar zuwa ranar 14 ga Afrilu, sai dai za a ci gaba da tsare su har sai sun cika sharuddan belin.

A ƙasar United States, an gano wani jirgin ruwan soji mai ƙarfin nukiliya nau’in Ohio-Class SSGN yana kusa da mashigar S...
01/04/2026

A ƙasar United States, an gano wani jirgin ruwan soji mai ƙarfin nukiliya nau’in Ohio-Class SSGN yana kusa da mashigar Strait of Gibraltar, wadda ke zama babbar kofar shiga zuwa Tekun Mediterrenean da yankin Gabas ta Tsakiya.

Rahotanni sun ce ana zargin jirgin na cikin USS Ohio, kuma yana gudanar da ayyukan dabaru a yankin.

Wannan motsi ya ja hankalin duniya saboda irin muhimmancin irin waɗannan jiragen ruwa a rundunar sojin ruwan Amurka, domin ana yawan tura su zuwa muhimman ayyukan soja na musamman.

An bayyana cewa daga cikin jiragen Ohio-class guda 18, guda 4 ne kaɗai aka sauya su zuwa wannan nau’i na SSGN, masu iya ɗaukar makamai har zuwa makamai masu linzami (Tomahawk) guda 154.

Haka kuma, ana amfani da wannan dandali wajen tallafa wa rundunonin soji na musamman, lamarin da ya sa ake hasashen cewa Washington na iya shirin wasu ayyukan ɓoye a ƙarƙashin ruwa yayin da rikice-rikice ke ƙara tsananta.

Za mu kawo ƙarshen yaƙin Iran ko da yarjejeniya ko babu - TrumpShugaban Amurka, Donald Trump ya nuna cewa yana son ya ra...
01/04/2026

Za mu kawo ƙarshen yaƙin Iran ko da yarjejeniya ko babu - Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya nuna cewa yana son ya rage hare-haren da ake kai wa Iran, yana mai alƙawarin cewa yaƙin zai zo karshe a cikin mako biyu ko uku masu zuwa ko da an cimma yarjejeniya ko ba a cimma ba.

Ya ce yanzu Iran tana da sababbin shugabanni waɗanda s**a fi sauƙin samu, ba masu tsattsauran ra'ayi ba kuma wadanda s**a fi magabatansu hankali.

Ya ce gwamnatin Amurka ta cimma burinta, duk da cewa ba ta iya kwace mashigar Hormuz ba daga hannun Iran. Yuwuwar ci gaba da karancin mai, farashin danyen man ya kara tashi a yau Laraba.

To amma kuma Mista Trump ya ce nan gaba kadan farashin zai sauka. A yau zai gabatar da jawabi ga al'ummar kasar ta Amurka ta talabijin.

Address

Giade Local Government
Bauchi
2023

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Giade Daily Post posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Giade Daily Post:

Share