16/07/2025
QANWATA.
Ko kinsan Nagartaccen NAMIJI bashi da LOKACIN yi miki QARYA?
May be ya miki ýar qaryar "baya iya cin Abinci ko Barci saboda bai ji muryar ki ba (Yana faruwa ga qalilan), ko idan ya rasa ki baxai Rayu ba!
Amma Shi maqaryaci kisa a Ranki ba abin da bazai iya furtawa ba, daga ciki zai iya cewa ma "Idan bai Aure ki ba shi da Aure sai a Lahira, idan kika tsaya wasa ma a gaban ki xai ďaura Aure da wata ba ke ba, kina nan a raye ke bai Aure ki ba, harma sai ki sai ki ganshi da ýaýa 5 yana faďa miki zaman dole yake da ita, akwai wasu kudi ne da yake jira da sun zo sai maganar Auren ku, kuma a hakan har ki kori wani a kansa🤔
Idan kuma Allah ya nufe ki da Hankali idan ya fara irin wannan sumbatun bayan ya taka miki tabargazar, sai kice a zuciyar ki "Wai don Allah wannan yaushe zai girma ya daina Qarya? saboda ya sha ki kin warke, a shawara Qanwata ma wanda ya miki wannan bai ma kamata ya dinga samun LOKACIN KI ba😊 bai ma Kamata daga sanda yayi Aure ace kina ma da Lambar sa kwance a cikin wayar ki ba😊 b***e wani Hoton sa ko saqon sa, na ďauka xaki ce "Allah yasa haka shi yafi Alkhairi a gareni, Allah ya kawo min wanda ya fishi Alkhairi, na ďauka ko Inuwarsa kika gani za kiyi ta kanki ne ki tsere??
Qanwata ba ina nufin Nagartattun basa Qaryar kare kai ko qaryar kula da shukar su ba, amma Namiji me Nagarta yana yin komai cikin bin maganar sa da AIKI ba a Baki kaďai ba, AIKI shi yake tabbatar da furuci Qanwata, ki lura! Kuma Nagartacce shi da AURE yake zuwa kuma ya gina matakan AURE.
Ki yi Addu'a Qanwata, domin shi mayaudari
yafi zuma zaqin zance, Allah ya zaba Alkhairi.
Zoohrah Oummu Deederht