Katagum Dailypost

  • Home
  • Katagum Dailypost

Katagum Dailypost Labarai Da Zarar Sun Faru

ALLAHU AKBAR: An kammala binne gawar marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura jihar Katsina.
15/07/2025

ALLAHU AKBAR: An kammala binne gawar marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari a Daura jihar Katsina.

Shugaba Tinubu Ya kar6i Gawar Tsohon Shugaban kasa Muhammad Buhari a KatsinaShugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi gaw...
15/07/2025

Shugaba Tinubu Ya kar6i Gawar Tsohon Shugaban kasa Muhammad Buhari a Katsina

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya karɓi gawar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, a Filin Jirgin Sama na Ƙasa da Ƙasa na Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina, a yau Talata, kafin a kammala jana’iza da sauran hakkokin ƙarshe a garin Daura.

Shugaba Tinubu ya sauka daga Abuja da misalin ƙarfe 1:42 na rana, inda ya duba jerin girmamawa na sojoji kafin jirgin rundunar sojin sama da ke ɗauke da gawar Buhari ya sauka daidai ƙarfe 1:51. Tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya rasu ne ranar Lahadi, 13 ga Yuli, 2025, a wani asibiti da ke birnin London.

Gawar Buhari ta iso tare da uwargidansa Aisha Buhari, Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Ƙasa Femi Gbajabiamila, da sauran ‘yan uwa da makusanta. Shugaban ƙasa Tinubu tare da Mataimakinsa Shettima, Shugaban ƙasar Guinea-Bissau Umaru Sissoco Embaló, Firayim Ministan Jamhuriyar Nijar Ali Lamine Zeine, tsohon shugaban Nijar Issoufou Mahamadou da tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa Yemi Osinbajo sun tarbi akwatin gawar a bakin jirgin.

Wata tawagar manyan hafsoshin soja guda tara ne s**a ɗauki akwatin gawar da aka lullube da tutar Najeriya cikin girmamawa, wanda s**a haɗa da manyan hafsoshin soja, sojojin ruwa da na sama.

Shikenan an tafi da gawar tsohon shugaban kasa zuwa mahaifarsa ta Daura domin biznewa
15/07/2025

Shikenan an tafi da gawar tsohon shugaban kasa zuwa mahaifarsa ta Daura domin biznewa

An fito da gawar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga cikin jirgi.
15/07/2025

An fito da gawar shugaban kasa Muhammadu Buhari daga cikin jirgi.

YANZU-YANZU: An fito da gawar Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga cikin jirgi idan za'a wuce da ita Daura.
15/07/2025

YANZU-YANZU: An fito da gawar Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari daga cikin jirgi idan za'a wuce da ita Daura.

Yanzu za'a fito da gawar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
15/07/2025

Yanzu za'a fito da gawar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alh Atiku Abubakar Ya isar Daura don tarbar gawar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
15/07/2025

Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Alh Atiku Abubakar Ya isar Daura don tarbar gawar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

CIKIN HOTO: Shugaba Tinubu ya sauka a jihar Katsina domin tarbar gawar shugaban kasa Muhammadu Buhari.
15/07/2025

CIKIN HOTO: Shugaba Tinubu ya sauka a jihar Katsina domin tarbar gawar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ana ci gaba da tona kabarin marigayi Tsohon Shugaban kasa Muhammad Buhari a gidansa da ke daura.
15/07/2025

Ana ci gaba da tona kabarin marigayi Tsohon Shugaban kasa Muhammad Buhari a gidansa da ke daura.

HOTUNA: Yadda al’ummar jihar Gombe s**a yi wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari Salatul Gha’ib a yau Talata a cikin ...
15/07/2025

HOTUNA: Yadda al’ummar jihar Gombe s**a yi wa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari Salatul Gha’ib a yau Talata a cikin garin.

Hotuna: 📸 Abba Sani Pantami

Somewhere in Nigeria 🇳🇬♥️
15/07/2025

Somewhere in Nigeria 🇳🇬♥️

DA DUMI-DUMI: Mata masu zaman makoki ke yin karatun Al-Qurani a gidan marigayi Muhammadu Buhari dake Daura, jihar Katsin...
15/07/2025

DA DUMI-DUMI: Mata masu zaman makoki ke yin karatun Al-Qurani a gidan marigayi Muhammadu Buhari dake Daura, jihar Katsina, gabanin isowar gawar mamacin.

Address

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Katagum Dailypost posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Contact The Business

Send a message to Katagum Dailypost:

Shortcuts

  • Address
  • Telephone
  • Alerts
  • Contact The Business
  • Claim ownership or report listing
  • Want your business to be the top-listed Media Company?

Share