Darus Sunnah TV

Darus Sunnah TV QUR'AN AND SUNNAH

08/10/2026

Kai
Daga

Masjidu Dan Malam Hanyar Jos Bauchi,

KARATUN LITTAFIN
Muhktasar Addà'u Waddawà'u.

Tare da
Malam Ibrahim AbdurRAHMAN Al'hanafı (Abu Aneesah

07/10/2026
07/10/2026

Kai
Daga

Masjidu Dan Malam Hanyar Jos Bauchi,

TAFSEER SURATU
Al-Mulk

Tare da

Malam Sulayman Zakariyya

07/10/2026

Karatun Mata

SHEIKH MAHMOOD IBRAHIM SHIRA

07/10/2026

KARATUN MATA

Sheikh Mahmood Ibrahim Shira

06/10/2026

Kai
Daga

Masjidu Dan Malam Hanyar Jos Bauchi,

KARATUN LITTAFIN
Umdatul-Ahkàm

Tare da

Malam Muhammad Shamsuddeen Muhammad

MALAMAI SAMA DA 1,000 SUN TARU A KANO, SUN FITAR DA MATSAYA KAN SHUGABANCIN TINUBU DA 2027Sama da malamai 1,000 daga jih...
05/10/2026

MALAMAI SAMA DA 1,000 SUN TARU A KANO, SUN FITAR DA MATSAYA KAN SHUGABANCIN TINUBU DA 2027

Sama da malamai 1,000 daga jihohi 19 na Arewacin Najeriya ne s**a taru a Kano, inda s**a yi nazari kan halin da ƙasar ke ciki a ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, tare da bayyana matsayarsu kan zaɓen 2027.

Taron wanda aka yi wa taken “Nazari kan Halin da Ƙasa ke Ciki a Zamanin Shugaba Tinubu da Zaɓen 2027”, ƙungiyar Ko Da Naka ce ta shirya shi tare da haɗin gwiwar AFAQ Educational Foundation, a ranar Lahadi, 4 ga Oktoba, 2026.

Ko Da Naka ƙungiya ce mai fafutukar samar da shugabanci nagari da ci gaban al’umma, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Kabir Bashir Abdulhamid. Duk da cewa harkokin siyasa na daga cikin abubuwan da take mayar da hankali a kai, amma ƙungiyar ba ta jingina kanta da wata jam'iyya, manufarta ita ce ta duba mutanen da take ganin sun cancanta a jam’iyyu daban-daban, ta ƙarfafa su.

Manyan malamai da masana daga sassa daban-daban na Arewa sun halarci taron. Daga cikinsu akwai Prof. Muhammad Muslim Ibrahim, Dr. Abdulmuddalib Ahmad Gidado, Barrister Ibrahim Sabi’u Jibiya, Dr. Umar Datti, Dr. Aminu Ismail Sagagi, Dr. Umar Dokaji Gombe da Dr. Nura Musa Kaduna.

A taron, an gabatar da takardu guda bakwai da s**a taɓo manyan matsalolin da ake taƙaddama a kansu a Najeriya a yanzu.

Alhaji Ahmad Yahuza Getso ya gabatar da takarda kan matsalar tsaro a Najeriya, yayin da Barrister Elzubair Abubakar ya yi bayani kan matsin rayuwa da na tattalin arziki a ƙarƙashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.

Dr. Abubakar Muhammad Ali ya gabatar da tasa takardar ne kan ƙarin haraji a gwamnatin Tinubu, yayin da Dr. Najibullah Abdallah Nuhu ya yi magana kan hijirar ƙwararru daga Najeriya da illar hakan ga ƙasa.

Batun rawar da malamai ya kamata su taka shi ma ya samu kulawa a taron, inda Dr. Abdulmuddalib Ahmad Gidado ya gabatar da takarda kan matsayin malamai a cikin al’umma da tasirinsu wajen tsayuwar gaskiya da adalci.

Prof. Muhammad Muslim Ibrahim kuwa ya yi magana kan zaɓen ɗan takara bisa cancanta ba bisa jam’iyya ba, yayin da Prof. Umar Adam Gombe ya gabatar da takarda kan darussan da za a koya daga mulkin Tinubu.

Bayan waɗannan jawabai da tattaunawa, mahalarta taron sun fitar da takardar bayan taro wadda ta nuna cewa manyan abubuwan da s**a fi damunsu su ne halin tattalin arziki, rashin tsaro, ficewar ƙwararrun ’yan Najeriya zuwa ƙasashen waje, rawar malaman addini da kuma zaɓen 2027.

A batun tattalin arziki, taron ya soki janye tallafin man fetur, sauya tsarin canjin Naira, ƙarin kuɗin wutar lantarki da sauye-sauyen haraji.

Mahalarta na ganin waɗannan manufofi sun ƙara jefa talaka cikin kuncin rayuwa, musamman a daidai lokacin da ake fama da tsadar kayayyaki da rashin aikin yi. A nan ne s**a ce muddin gwamnati ba ta sauya manufofin da suke ganin sun jefa jama’a cikin wahala ba, ba su ga dacewar a sake zaɓenta a 2027 ba.

Malaman sun nuna damuwa kan kashe-kashe, garkuwa da mutane da ayyukan ’yan bindiga da ake fama da su, musamman a Arewa maso Yamma. Sun buƙaci gwamnatin tarayya ta ɗauki matakan gaggawa domin kawo ƙarshen matsalar.

Bayan haka, takardar bayan taron ta ce idan matsalar tsaro ba ta samu mafita ba, Shugaba Tinubu ya haƙura da neman wa’adi na biyu; idan kuma ya tsaya takara, s**a yi kira ga ’yan ƙasa kada su sake zaɓensa. Wani abin da malaman s**a ce yana ci musu tuwo a ƙwarya shi ne yadda ƙwararrun ’yan Najeriya ke barin ƙasar.

Sun ambaci likitoci, malamai, injiniyoyi da sauran ƙwararru waɗanda ke fita don yin aiki a ƙasashen waje, suna masu danganta hakan da rashin aikin yi, ƙarancin kayan aiki, rashin kyakkyawan yanayin aiki da kuma matsin tattalin arziki.

Sun nemi gwamnati ta inganta albashi da yanayin aiki, sannan ta samar da hanyoyin da za su ƙarfafa wa waɗanda s**a yi hijira gwiwar dawowa gida.

A cewarsu, idan gwamnati ta kasa yin hakan kafin 2027, wannan ma wani dalili ne da ya sa suke ganin ya kamata a sauya ta.

Mahalarta taron sun kuma yi kira ga malaman addini da su guji zama ’yan barandan siyasa, su riƙa faɗa wa masu mulki gaskiya, su yaba idan an yi abin kirki, sannan su soki abin da bai dace ba.

A cewarsu, bai kamata jam’iyya, ɓangare ko addinin wanda yake kan mulki ya hana malami tsayawa kan abin da yake ganin gaskiya da adalci ba.

Da yake karanta jawabin bayan taron a madadin mahalarta, Sheikh Kabir Bashir Abdulhamid ya bayyana taron a matsayin na kishin ƙasa da tsayawa kan gaskiya, yana mai jan hankalin ’yan uwansa malamai kada su sayar da mutuncinsu da imaninsu saboda abin da ya kira “na goro” wajen kare abin da suke ganin zalunci ne.

Amma duk da kakkausar s**ar da aka yi wa gwamnatin Tinubu, saƙon taron kan 2027 bai tsaya ga Tinubu kaɗai ba.

Mahalarta sun ce abin da ya kamata ’yan Najeriya su duba shi ne cancantar mutum, ba jam’iyyarsa ba.
Sun ce makomar Najeriya ta fi kowace jam’iyya, ƙabila ko yanki muhimmanci, don haka ya kamata a tantance duk mai neman mulki ta fuskar ƙwarewa, gaskiya, cancanta da manufofin da yake son aiwatarwa.

A taƙaice, suna son a zaɓi wanda zai iya kawo sauƙin rayuwa, tsaro, aikin yi, adalci da ci gaba, ko daga wace jam’iyya, ƙabila, yanki ko addini ya fito.

Shin kun yarda da matsayar waɗannan malamai? Kuma idan zaɓen 2027 ya zo, wane abu ne zai fi tasiri wajen zaɓinku: jam’iyya, ɗan takara, ko yadda gwamnati mai ci ta gudanar da mulki?

04/10/2026

Karatun Nurses Quarters

04/10/2026

Sheikh Mahmood Ibrahim Shira

Address

Ajiya Adamu Road Opposite Central Market Bauchi
Bauchi
740101

Telephone

+2347033195330

Website

Alerts

Be the first to know and let us send you an email when Darus Sunnah TV posts news and promotions. Your email address will not be used for any other purpose, and you can unsubscribe at any time.

Shortcuts

Share

Category